✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya yi tattakin kilomita 450 bayan sa-in-sa da matar sa

Wani mutum wanda ya fito daga gida domin sararawa bayan wata sa-in-sa da matarsa ya bige da yin tattakin kilomita 450 a kafa.

Wani mutum dan kasar Italiya wanda ya fito daga gida domin sararawa bayan wata sa-in-sa da matarsa ya bige da yin tattakin kilomita 450 a kafa.

Tuni dai ‘yan kasar suka fara yi masa lakabi ta kafafen sada zumunta na zamani da sunan wani jarumin fim mai suna “Forrest Gump” wanda ya yi tattakin dubban kilomitoci a kasar Amurka a shekarar 1994.

‘Yan sandar kasar ne dai suka taka masa birki a wani gari mai suna Fano da misalin karfe 2:00 na dare, mako daya bayan ya bar garin Como dake arewacin kasar.

An dai ci tarar mutumin mai kimanin shekaru 48 Dalar Amurka 485, kwatankwacin sama da N200,000 saboda karya dokar kullen kasar.

Wata jaridar kasar mai suna Resto del Carlino ce dai ta fara bayyana labarin kafin daga bisani ya bazu a kafafen watsa labarai na kasar.

Wasu da dama daga masu tsokaci a kafafen sada zumunta sun bayyana mutumin a matsayin jarumi, yayin da suka yi Allah-wadai da tarar da aka lafta masa.

Wani ma cewa ya yi kamata ya yi a karrama shi ba wai a ci shi tara ba, tare da ba shi kyautar sababbin takalma, wani kuma ya yaba masa saboda huce takaicinsa ta hanyar tattakin a maimakon tayar da zaune tsaye.

Mutumin ya shaida wa ‘yan sandan cewa, “A kafa na zo nan, ban yi amfani da kowanne irin abin hawa ba.

“Na hadu da da mutane a hanya da suka bani gudunmawar abinci da kayan sha.

“Na gaji tibis gaskiya, amma lafiya ta kalau, babu inda yake min ciwo,” inji shi.

Mutumin dai ya ce ya kan yi tafiyar da ta kai ta kimanin kilomita 60 a kowacce rana.

‘Yan sanda dai sun cafke shi ne da tsakar dare lokacin da yake tsaka da tafiya a kan wata babbar hanya.

Daga bisani ne bayan sun duba takardar shaidar sa suka gano cewa matarsa ta jima da bayar da cigiyar batansa, inda nan take suka tuntube ta ita kuma ta zo ta tafi da shi.

%d bloggers like this: