✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya mutu lokacin da ya sa agolansa ya harbe shi don gwajin maganin bindiga

Wani uba ya mutu lokacin da ya sa agolansa ya harbe shi da bindiga don gwajin maganin bindigar a kansa. Rahotanni sun ce Yusif Adamu…

Wani uba ya mutu lokacin da ya sa agolansa ya harbe shi da bindiga don gwajin maganin bindigar a kansa.

Rahotanni sun ce Yusif Adamu ya umarci agolansa, mai suna Suugbomsumen Adamu ya harbe shi ne domin gwajin ingancin wasu sababbin hade-haden sauwoyi da ya samu da nufin kare shi daga harbin bindiga.

An ce marigayin ya yi kurin cewa sauwoyin da ya sha suna da karfi kuma za su kare shi daga harbin bindiga; don haka ya umarci agolan ya harbe shi saboda ya san bindigar ba za ta kama shi ba.

Sai dai agolan na sakin bindigar ga Adamu, sai aka ga ya fadi kasa a mace.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi iinda ta ce lamarin ya faru ne a kauyen Sankipo da ke karamar Hukumar Jada, kuma ta ce agolan yana hannunta.

Kakakin Rundunar, SP Suleiman Nguroje ya ce, “An kama wanda ya harbe shi, kuma ’yan sanda za su binciki lamarin sosai tare da gabatar da batun a gaban kotu.”