✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kirkiri gida mai juyawa don ya burge matarsa

Ya shekara shida yana gina gidan don matakarta ta kashe kwarkwatar idonta.

Wani dattijo mai shekara 72 ya kirkiri gida mai juyawa domin burge matarsa da ke matsa masa lamba a kasar Bosnia.

Vojin Kusic ya ce tsabar gunagunin da matarsa ke yawan yi masa na neman ya rika sauya fasalin gidansu domin ta rika samu tana ba wa idanunta abinci ta hanyar ganin irin abin da ke faruwa a waje ne ya sa shi zama mai kirkira, karfi da yaji.

Dattijon ya ce yawan tereren da matar tasa ke yi ya sa shi tunanin yadda za a yi ya mayar da gidan nasu ta yadda zai rika juyawa ta kowace kusurwa, domin matar ta samu ta rika kashe kwarkwatar idanunta.

“Gajiya na yi da yawan gunaguninta a-kai-a-kan cewa a sauya fasalin gidanmu, shi ne na ce, ‘To bari zan gina miki gidan da zai rika juyawa saboda ki rika juya shi yadda kika ga dama’,” inji shi.

Yanzu ya dai ya kirkiro ya kuma gina mata wani gida wanda za ta iya juya shi ta kowace kusurwa ta ga duk abin da take son gani a waje, daga duk inda take a cikin gidan.

Da yake bayanin yadda gidan yake, Mista Kusic ya ce, “Idan aka rage gudunsa zuwa karshe, gidan zai dauki awa 24 yana tafiya har ya juyo zuwa daidai inda ya fara tafiya.

“Idan aka kure gudunsa kuma, a cikin dakika 22 gidan zai iya juyawa zuwa daidai inda ya fara tafiya.”

Mista Kusic, wanda mutane suke tururwar zuwa ganin gidan da ya gina wa matar tasa a halin yanzu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa shi ba injiniya ba ne, kuma ba shi da wata kwarewa a fannin kirkira.

Ya ce, hasali ma bai halarci wata makarantar ku-zo-ku-gani ba saboda gidansu talakawa ne, shi kuma a matsayinsa na talaka dole ya nemo yadda zai rika yi wa kansa abin da yake bukata.

A cewarsa, gidan da ya gina zai iya jure karfin girgizar kasa fiye da gidajen da ke tsaye a wuri daya.

A cewarsa, kirkirar da wasu ’yan asalin Bosnia mazauna Amurka masu kirkira, Nikola Tesla da Mihajlo Pupin, suka yi ta ba shi kwarin gwiwa cewa talauci da rashin iliminsa ba za su hana shi kirkiro wani abu na.

Kowanne daga cikin Telsa da Pupin masanin kimiyya ne da ya kirkiro abubuwan da har yanzu duniya ke amfani da su a fannin kimiyyar sadarwa da kuma samar da wutar lantarki.

“Ni ba na ganin sa a matsayin kirkira, ilimi da karfin azama kawai abin ke bukata, sannan ina da lokaci da ilimi daidai gwargwado,” inji Kusic.

Reuters ta so jin ta bakin matarsa kan wannan kirkira da ya yi domin ya burge ta, amma matar ta ki cewa komai.

Mista Kusic ya ce shi da kansa ya gina daukacin gidan a tsawon shekara shida, in banda lokacin da aka kwantar da shi a asibiti saboda ciwon zuciya.

Ya ce a lokacin da yake kwance a asibiti, “Na roki likitoci su yi yadda za a yi in rayu na karin akalla shekara daya domin in samu in kammala wannan aiki, saboda… babu wanda ya san yadda zai kammala shi.