✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe matarsa mai juna biyu a gadon asibiti

’Yan sanda sun cafke magidanci bisa zargin sa da kashe matarsa mai juna biyu a gadon aisibiti

’Yan sanda sun cafke wani magidanci bisa zargin sa da kashe matarsa mai juna biyu a kan gadon asibiti.

An tsare magidancin ne bayan da ya tumbuke na’urar Oksijin da aka sanya wa matar tasa a lokacin da aka kwantar da ita a asibiti.

“Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya ba da umarnin sashen binciken kisa ya bincike shi a  Sashen Bincikin Manyan Laifuka (CID),” inji kakakin ’yan sandan  Jihar Legas, Muyiwa Adejobi.

Ya ce an kwantar da matar a gadon asibiti ne sakamakon matsalar juna biyun da take dauke da shi, lokacin da mijin ya faki ido ya tumbuke mata Oksijin din, har ta kasa numfashi, daga baya ta rasu.

Ana kuma zargin cewa kafin faruwar lamarin, mutumin na da dabi’ar yawan dukan matar tasa.