✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya kashe kawunsa kan zargin maita a Adamawa

Wani mutum ya kashe kawunsa kan zargin maita a yankin Dumna Zarbu da ke Karamar Hukumar Guyuk ta Jihar Adamawa.

Wani mutum ya kashe kawunsa kan zargin maita a yankin Dumna Zarbu da ke Karamar Hukumar Guyuk ta Jihar Adamawa.

Wanda ake zargin mai shekaru 42 dai ya musanta aikata laifin da aka gurfanar da shi a kai.

Shaida sun ce  mamacin ya rasu ne bayan dan nasa ya buge shi da sanda saboda an zarge shi ne da kisan wasu mutane ta hanyar maita, zargin da ya musanta.

Bayan sauraron karar ne alkali Alheri Ishaku ta babbar kotun majistare ta daya da ke Yola ta ba da umarnin tsare wanda ake zargi da kisan a gidan yari.

Daga nan ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Janairu, 2024.