✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatun da suka fi samun kudi a kasafin 2024

A karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kudaden da Tinubu ya ware wa ma'aikatu da sauran bangarori a kasafin shekarar 2024

A karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kudaden da aka ware wa ma’aikatu da sauran bangarori a kasafin shekarar 2024 da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.

A ranar Laraba Tinubu ya gabatar da kasafin na Naira tiriliyan 27.5, ba tare da bayanin kason da ware wa ma’aikatu da bangarori ba, lamarin da ya sa ’yan Najeriya guna-guni.

Sanatoci sun nuna damuwa kan rashin samun karin bayanin kasafin, inda suka bukaci a dakatar da nazarinsa har sai an kawo bayanan.

Sai dai duk da haka Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan kasafin, washegari da dare Kwamitin Kasafi ya fitar da bayanin abin da ma’aikatu da bangororin za su samu.

Ga jerin ma’aikatun da suka samu kaso mafi tsoka:

  1. Ma’aikatar Tsaro: Naira biliyan 308.2
  2. Ma’aikatar Ayyuka: Naira biliyan 521.3
  3. Ma’aikatar Kudade: biliyan N519.9
  4. Ma’aikatar Lafiya: Biliyan N304.4
  5. Ma’ikatar Ilimi: Biliyan N265.4
  6. Ma’aikatar Wutar Lantarki: Biliyan N264.2
  7. Kamfanoin Gwamnati: Biliyan N820.9
  8. Ausun Manyan Makarantu (TETFund): Biliyan N665
  9. Ma’aikatar Gidaje: Biliyan N96.9
  10. Ma’aiatar Ruwa: Biliyan 87.7
  11. Ma’aikatar ’Yan Sanda: Biliyan N69.
  12. Majalisar Dokoki: Biliyan 198
  13. Ma’aikatar Neja Delta: Biliyan 324.8
  14. Hukumar UBEC: Biliya 251.4
  15. Hukumar Shari’a: Biliyan 165
  16. Hukumar Arewa maso Gabas: Biliya 126
  17. Asusun Kula da Lfiya a matakin farko: Biliyan 125.7.