✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ci tarar gwamnan Kano N25m kan zargin Alhassan Doguwa da kisa

Babbar Kotun Tarayya ta hana Gwamnan Kano sake bincikar zargin Alhassan Ado Doguwa da laifin kisa

Babbar Kotun Tarayya ta ci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tarar Naira miliyan 25 kan haddasa damuwa ga Honorabul Alhassan Ado Doguwa.

Kotun da ke zamanta a Abuja ta kuma soke umarnin da gwamnan ya ba wa Antoni-Janar na Jihar Kno na sake duba shari’ar zargin Alhassan Doguwa kan zargin kisa.

A zaman kotun na ranar Juma’a, Mai Shari’a Donatus Okorowo, ya umarci gwamnan kada ya sake “taba ’yancin dan Adam na mai kara (Alhassan Ado Doguwa) ko tsoma baki a abin da ya shafe shi.”

Alhassan Doguwa ya garzaya kotun ne bayan Gwamna Abba ya bukaci Antoni Janar na Jihar Kano ya sake waiwayar zargin da ake masa da kisan wasu mambobin Jam’iyyar NNPP a lokacin zabe.

A ranar 28 ga watan Fabrairu ne ’yan sanda suka tsare Alhasssan Ado Doguwa, a filin jirgi na Malam Aminu Kano a lokacin yana hanyarsa ta zuwa Umara.

Tsarewar na da alaka da zargin da ake masa da jagorantar ’yan daba da suka kona sakatariyar Jam’iyyar NNPP tare da kashe mutum biyu a mazabarsa.

Doguwa da ke wakiltar Doguwa/Tundun Wada a Majalisar Tarayya ya musanta zargin, wanda a kansa aka gurfanar da shi a kotu a Kano a watan Maris.

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta ba da umarnin tsare shi a gidan yari kafin daga baya ta ba da belinsa a kan Naira miliyan 500.

Daga bisani masu shigar da kara suka janye zarge-zargen tare da cewa, “ba mu samu gamsassun hujjojin da ke danganta Alhassan Doguwa da lafin ba.