Kungiyar matasa magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, (NYFA) ta bukaci Shugaba Tinubu ya gaggauta sauka daga mulki, saboda rashin sanin makamar aiki.
Kungiyar NYFA, ta yi wannan kira ne saboda abin da ta kira, “matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya a mulkinTinubu , wanda ba a taba ganin irinsa ba.
Daraktan yada labaran NYFA, Dare Dada, ya ce hauhawar farashin kayan masarufi da na lantarki da karancin man fetur da na takardar faso da kuma rashin aikin yi baya ga tabarbarewar bangaren kiwon lafiya da ilimi da tsaro, sun nuna gazawar Shugaba Tinubu.
Dare Dada ya kuma koka abin da ya kira gazawar gwamnatin Tinubu wajen magance matsalolin da ke ci wa miliyoyin ’yan Najeriya tuwo a kwarya ko daukar matakin da ya dace a kansu.
Don haka kungiyar ke kira ga shugaban kasan “ya sauka daga kujerarsa, tunda ya kasa magance matsalolin.
Da yake nuna fushin kungiyar bisa yadda gwamnatin ke tunkarar masalolin kasar, Dare ya ce, Najeriya ba ta taba samun koma bayan arziki a kowane bangare ba kamar a mulkin Tinubu.