Dan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 da ya wuce, ya ce kamata ya yi matasan Najeriya a yanzu, su jagoranci gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyyar Najeriya, don kuwa su ne suka fi ruwa da tsaki, a kan masu shekaru irinsa.
Ya ce dole ne dimokraɗiyyar Najeriya ta kasance mai ma’ana, kuma ginshiƙi mai ƙarfi. “Sama da komai, dole ne a aiwatar da ita ta hanyar zaɓuka na gaskiya da adalci, da za su mutunta ƙudurin al’umma.”
- Mutum 14 sun mutu, 50 sun jikkata a hatsarin jirgin kasa a Indiya
- Ra’ayin ƴan Najeriya game da mulkin Cif Ernest Shonekan
Atiku Abubakar, wanda ya bayyana haka ranar Litinin a taron manema labaran da ya gudanar a Abuja, babban birnin kasar game da halin da kasar ke ciki, ya kuma ba da labarin yadda aka taba yunkurin hallaka shi a fafutukar da yake yi wajen tabbatar da mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.
Atiku ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, sai dai ya garzaya kotu don kalubalantar nasarar Tinubu.
A Alhamis din makon jiya ce Kotun Koli ta yi watsi da karar da ya shigar tana mai cewa ba shi da gamsassun hujjojin da za su sa a soke zaben Shugaba Tinubu.
Amma a taron da ya gudanar ranar Litinin, Atiku ya ce ba zai daina gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya a kasar ba.
“A gare ni da kuma jam’iyyata wannan babi na gwagwarmayarmu ya zo karshe. Sai dai ba wai na tafi kenan ba.
‘Ya kamata a kammala duk wata shari’ar zabe kafin rantsuwa’
Ya ce abu na gaba shi ne dole ne a yi tanadin cewa duk wata shari’ar zaɓe sai an kammala ta, kafin a rantsar da mutumin da ya lashe zaɓen da aka yi.
A cewarsa, irin wannan tsarin Najeriya ta yi amfani da shi a 1979. “Lokacin da ake ɗauka tsakanin zaɓuka da rantsar da waɗanda suka ci zaɓe, ya yi kaɗan a iya kammala shari’o’in zaɓe.”
A cewarsa abin da ake da shi yanzu, daidai yake da cewa ɓarayi su riƙe abin da suka sata, kuma su yi amfani da dukiyar wajen kare kansu a gaban shari’a.
“Kawai yana ƙarfafa gwiwar fashin ƙuri’un mutane ne, maimakon hana yin hakan.”
Ba zan daina gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya ba — Atiku
Atiku Abubakar ya ce muddin yana numfashi ba zai daina fafutukar dabbaka dimokuradiyya a ƙasar ba.
“Muddin ina numfashi zan ci gaba da gwagwarmaya tare da sauran ‘yan Nijeriya, don karfafa dimokuradiyya da tsarin doka da kuma yin garanbawul ga tsarin siyasa da tattalin arziki da kasarmu ke bukata don cimma ainhin abin da take da damar yi.
“A yanzu matasanmu ne za su jagoranci wannan gwagwarmayar, wadanda sun ma fi mu damar yin hakan.
“A ko da yaushe ina zaben ‘yanci maimakon bauta, ko da kuwa wannan zabin ba zai yi mini dadi ba. Lokacin da na shiga siyasa, babban kalubale shi ne a kori sojoji daga mulki yadda za a dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.
Ya kara da cewa: “Daga baya hakan ya zama wani abu da zai zama fafutuka mai tsawo, kuma a matsayina na daya daga cikin shugabannin fafutukar, an taba neman halaka ni.
Kan labarin yunƙurin kashe shi da aka yi, Atiku ya bayyana cewa an kashe ‘yan sanda tara da ke “gadin gidana na Kaduna a yunkurin halaka ni. An tilasta mini yin gudun hijira na wata tara,” in ji Atiku Abubakar.
‘Martani kan ƙalubalen da na yi ta fuskanta’
A martanin da na mayar kan ƙalubalen da na yi ta fuskanta, na shigar da ƙararraki a kotuna, waɗanda suka yi nasarar samar da ɗaukar matakai masu cike da tarihi da suka taimaka wajen ƙarfafa dimokuraɗiyyarmu da dokokin shari’a.
A cikin wannan yanayi da ake ciki mai cike da tarihi, da zaɓi mafi sauƙi a gare ni shi ne bai wuce na ja da baya ba, bayan “fashin nasarata da APC da INEC suka yi min.”
“Amma na je kotunan Nijeriya don neman adalci, har kotun Amurka na je don ta taimaka wajen gano abin da hukumomin da alhakin hakan ya rataya a wuyansu a ƙasarmu suka kasa yi, ciki har da bankaɗo takardun shaidar karatun mutumin da aka rantsar a matsayin shugaban ƙasarmu, don a gano ko ainihin wane ne shi.
“Na gabatar da shaidar da na samo da taimakon Kotun Amurka ga Kotun Ƙolinmu don ta yi adalci a kan lamarin.
“Na ba da wannan bayanin ne don a gane cewa abin da a yanzu muke fama da shi ya fi gaban takarar shugaban ƙasa ɗaya ko biyu kuma ya fi Atiku Abubakar.
“Ba batu ne da ya ta’allaƙa a kaina ba; lamari ne da ya shafi ƙasarmu, Nijeriya. Batu ne na irin rayuwar da muke so mu bar wa al’umma mai zuwa da kuma irin misalin da muke so mu bar wa ƴaƴanmu da jikokinsu.