✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata gwamnati ta sassauta tatsar haraji a wurin ’yan Nijeriya — Sarki Sanusi II

Ya kamata gwamnati ta karɓi haraji domin ci gaban ƙasa, ba domin samun riba ba.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce ya kamata gwamnati ta riƙa cizawa tana hurawa game da haraje-harajen da take ƙaƙaba wa al’umma.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron  tattalin arziki da zuba jari na 2024 da aka gudanar a cibiyar taro ta Obi Wali da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.

Ya kafa hujja da maganar tsohuwar Firaiministar Birtaniya, Margaret Thatcher, wadda take cewa babu ƙasar da da za ta samar da ci gaba ta hanyar tatsar al’ummarta.

Ya ce duk da cewa karɓar haraji na da muhimmanci, amma bai kamata a tsawwala wa jama’a ba, “ya kamata gwamnati ta karɓi haraji domin ci gaban ƙasa, ba domin samun riba ba.”

A cewar tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, a zahirin gaskiya ƙasar nan na buƙatar sama da watanni shida ko shekara guda kafin a warware dagula tattalin arzikin da aka yi a shekaru goma da suka wuce.

Tun bayan hawansa karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fara kawo sauye-sauye da dama domin farfaɗo da tattalin arzikin kasar ciki har da cire tallafin man fetur da kuma haɗewar kasuwar canji.

Da yake jawabin, Sarki Sanusi ya bayyana cewa za a ɗauki lokaci kafin ‘yan Najeriya su fara jin tasirin wasu daga cikin waɗannan sauye-sauyen tattalin arziki.

Tsohon Gwamnan na CBN ya kuma ƙara da cewa, matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun zama tilas domin ɗora Najeriya a kan turbar bunƙasar tattalin arziki.