Kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da shugabannin sojoji da su gaggauta gurfanar da sojojin da ake zargi da kisan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Yobe, Sheikh Muhammad Goni Aisami.
Kungiyar ta JNI ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin ta hannun Babban Sakatarenta, Dokta Khalid Abubakar Aliyu, inda ta ce ba wai kawai a yanke hukuncin ba har ma da duba yadda aka yi kisan.
- DAGA LARABA: Yadda Rabon Gado Ke Neman Zama Tarihi
- Zan iya tuka mota daga Abuja zuwa Kaduna babu ’yan rakiya – Ministan Buhari
Kungiyar ta kuma ce ya kamata a yi amfani da irin hukuncin ga duk wani lamari makamancin haka a kasar nan, domin ya zama izina.
Sai dai ya ce bai kamata a ci gaba da yin tashe-tashen hankulan da ake tafka wa a kasar ba yana mai cewa, “Muna da tabbacin cewa wadannan kashe-kashen da ba su dace ba, galibi an yi tunanin aikata su ne.
“Kungiyar JNI ta yi matukar kaduwa da rahoton kisan da aka yi wa Sheikh Muhammad Goni Aisami tare da sace masa mota.
“A takaice dai, kisan Shehin Malamin abu ne mai ban tsoro, abin zargi, kuma abin Allah-wadai, idan aka yi la’akari da irin halin kirkin Malamin, wanda a ra’ayinsa ya bai wa maharan dama su hau mota daya,” inji JNI.