✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazauna gari sun kori Boko Haram bayan kashe kyaftin ɗin soja

Sarkin Gwoza Mohammed Shehu Timta ya ce ’yan ta’addan sun afka musu ne da ƙarfe 1:00 na dare.

Al’ummar garin Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun fatattaki ’yan ƙungiyar Boko Haram bayan kai musu hari a ranar Laraba.

Ƙungiyar ‘yan ta’addan ta kuma kashe wani kaftin ɗin soji a harbin na ba zata.

Sarkin Gwoza Mohammed Shehu Timta ya ce ’yan ta’addan sun afka musu ne da ƙarfe 1:00 na dare.

“Da gaske ne Boko Haram sun afka wa garinmu. Kuma an yi rashin sa’a wani kaftin ɗin soja ya rasa ransa.

“Jami’an tsaronmu na sa-kai sun samu nasarar kashe ‘yan ta’addan uku. Sauran sun gudu sun bar babura 10 da wasu makamai,” in ji shi.