A yau 5 ga watan Mayu 2025 tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya cika shekaru 15 da rasuwa.
’Yar’Adua wanda ya rasu a bayan dogaruwar jinya yana daga cikin daidaikun zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da talakawan kasar ke kewar su, saboda kyakkyawan kamun ludayin gwamnatinsa.
Sai dai kuma an lura cewa yawancin shugabannin da suka fi samun irin wannan yabo daga talakawan Najeriya, ba su fiye yin tsawon kwana ba, a kan mulki suka rasu.
Zuwa yanzu, shugabannin Najeriya huɗu ne suka mutu a kan mulki, kuma dukkansu daga yankin Arewa.
- Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato
- NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka
- Ya kamata a zuba jari a harkar noman rani — Zulum
Biyu daga cikinsu zaɓaɓɓu ne a karkashin tsarin dimokuradiyya — Marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, Fira Ministan kasar na farko, sai kuma Marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’adua.
Ragowar biyu kuma shugabannin mulkin soja ne — Janar Murtala Ramat Muhammad da kuma Janar Sani Abacha, waɗanda su ma suke shan ya yabo, duk kuwa da yadda ake wa gwamnatocin soji kallon masu takalmin karfe.
Zababbun shugabanni
1- Abubakar Tafawa Ɓalewa
Rasuwar Marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa na daga cikin abubuwan da suka fi girgiza Najeriya bayan samun ’yancin kanta daga turawan mulkin mallaka.
Sojoji ƙarƙashin Janar Aguiyi Ironsi ne suka kifar da gwamnatin su Tafawa Ɓalewa a juyin mulki a karon farko a tarihin Najeriya. Ko da yake a lokacin, Cif Nnamdi Azikiwe ne shugaban kasa.
A juyin mulkin na ranar 15 ga watan Janairu, 1966, sojoji suka sace Tafa Balewa daga gidansa da ke Legas, sai bayan kwanaki aka tsinci gawarsa a gefen hanya.
Juyin mulkin da kisan gilla da masu sojojin suka yi masa da wasu manyan shugabanni irin su Firimiyan Jihar Arewa, Alhaji Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya bar babban tabo a tarihin Najeriya, wanda daga bisani ya haifar da yaƙin basasa.
Tsare-tsaren Fira Minista Tafawa Balewa wanda zamaninsa ya ratsa mulkin mallaka zuwa bayan samun mulkin kan Njaeriya ya mayar da hankali ne wajen gina kasa da kuma daga darajar Najeriya a idon dunya.
A matsayinsa na jagoran majalisar ministoci ya jagoranci samar da kundin tsarin mulkin da ya mayar da Najeriya Jamhuriya a 1963 gami da soke tsarin mulkin sarauta da kuma Ofishin Gwamna-Janar a tsarin shugabancin Najeriya.
Ya kuma bayar da fifiko ga hadin kan al’ummar kasa ba tare da la’akari da bambancin kabila ko yanki ba. Haka kuma, kasancewarsa tsohon malamin makaranta, Tafawa Balewa ya mayar da hankali ga inganta ilimi da fadada samar da shi ga ’yan Najeriya a duk sassan kasar.
Domin bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasa kuwa, ya ba da muhimmanci ga fannin noma da kasuwanci da masana’antu da kuma jawo masu zuba jari daga ketare.
Aikin majalisar ministocinsa ce ya kai ga gina matatar mai ta farko a a Najeirya shekarar 1966, sa’annan ta samar da Madatsar Ruwa ta Kainji, domin noman rani da samar da wutar lantarki, da kuma samar da kamfanin sarrafa tama da dai sauransu.
A zamaninsa, Najeriya ta kasance abin girmamawa a idon duniya, hatta a taron Majalisar Dinkin Duniya, inda wannan tsohon malamin makaranta daga Jihar Bauchi da ma Najeriya sun kasance abin sha’awa ga turawa.
2- Umaru Musa ’Yar Aduwa
A ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010 Najeriya ta girgiza da labarin rasuwar shugaban kasarta, Alhaji Umaru Musa ‘Yar’Adua bayan fama da jinya.
Tun kafin zamansa shugaban a ranar 29 ga watan Mayun 2007, an yi masa dashen koda, lamarin da ya zama abin ce-ce-kuce a lokacin mulkinsa. A watan Satumban 2009 ya tafi kasar Saudiyya domin duba lafiyarsa, daga bisani aka sanar cewa yana fama da ciwon zuciya.
Dadewarsa yana jinya a kasar wace ta tare ya mika mulki ga mataimakinsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa ba ta haifar da rudani inda watan Fabrairun 2010 Majalisar Dokokin Najeriya ta yi amfani da karfinta ta ayyana mataimakinsa, Goodluck Jonathan a matsayin mukaddashin Shugaban Kasa.
A ranar 24 ga watan Fabarairu aka dawo da shi gida, amma Mukaddashin Shugaban kasa ya ci gaba da jan ragamar gwamnati.
Bayan watanni biyu, a ranar 5 ha watan Mayu Allah Ya yi masa cikawa, wanda haka ya ba damar rantsar da Jonathan a matsayin shugaban kasa.
Duk da rashin lafiyar Shugaba Yar’Adua ya samu farin jini a wurin al’ummar Najeriya musamman saboda manufofin gwamnatinsa 7 na 7 point Agenda, wadda ta mayar da hankali wajen inganta makamashi da wadata kasa da abinci da samar da arziki da inganta ilimi da tsaro da sufuri da mallakar kasa.
Ya yi zarra a dabi’arsa ta bin doka inda ya zaman shugaban kasa na farko da ya bayyana kadarorinsa ga al’ummar kasa. Uwa uba ya ba da umarnin sakin kudaden Gwamnatin Jihar Legas da gwamnatin Obasanjo ta ki saki daga Asusun Gwamnatin Tarayya
Haka kuma kokarinsa wajen magance matsalar rashin tsaro da fasa bututun mai a yankin Neja Delta, inda ya bullo da shirin afuwa da tallafi tubabbun tsagerun yankin da suka ajiye makamai, har ya samar da ma’aikatar Neja Delta domin bunkasa yankunan da ayyukan hakar danyen mai suka lalata.
Manyan abubuwan da ake tuna gwamantin Murtala da su sun hada da fara aikin dauke Babban Birnin Tarayya daga Legas zuwa Abuja kuma kirkiro sabbin jihohi bakwai (daga 12 zuwa 19) da nufin share hawayen kananan kabilu da kuma samar da daidaito a tsakanin al’ummar kasa.
Ya kuma kaddamar da shirin noma na Operation Feed the Nation domin habaka samar da abinci a kasa da kuma rage dogaro da kasashen waje wajen samun abinci.
Kazalika ya dauki matakai domin magance cin hanci da rashawa inda da kafa hukumar karbar korafe-korafen jama’a. Haka kuma ta yi gagarumin garambawul da nufin tsarkake aikin gwamnati inda sallami dubbabn ma’aikata a kokarinta na kawar da cin hanci a tsarin aikin gwamnati.
Gwamnatin Murtala ta bullo da tsarin da ya ba wa ’yan Najeriya damar mallaka da shiga a dama da su a harkokin tattalin arziki, wanda ya ba su samar mallakar kamfanoni da a baya baki ke mallaka.
Ya kuma taka rawar gani wajen gani kasashen Kudancin Afirka irin su Angola sun samu ’yancin kai, kamar yadda ta yi fito-na-fito da wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu.
Kazalika a zamaninsa, duk da takunkumin da manyan kasashe suka kakaba wa Najeriya, amma ya rage hauhawar farashin kayayyaki a cikin gida, da kuma basukan da ake bin Najeriya a kashen waje daga dala biliyan 36 zuwa biliyan 27. Ya ninninka yawan kudaden da ke asusun ajiyar kasashen waje na kasar daga dala miliyan 494 zuwa biliyan 9.6 sannan ya daidaita farashin canjin dala na tsawon lokaci a kan N80.
Gwamnatinsa ya murkushe masu tayar da kayar baya a cikin gida da kuma barazanar kasashen waje, sannan ta kama tare da tatsar wasu manyan mutane da suka durkusar da wasu bankunan kasuwanci.
Abacha ya kara yawan jihohi daga 30 zuwa 36, baya ga shirinsa na Vision 2010 mai nufin sanya Najeriya a sahun manyan kasashe a shekarar ta 2010.
A zamanin mulkinsa, ya takaita tafiye-tafiyensa ne zuwa kasashen Afirka, sannan ya yi tsayuwar daka wajen samar da tsaro a kasashen nahiyar da ke fama da yakin basasa, musamman a kasashen Laberiya da kuma Saliyo inda ya murkushe juyin mulki tare da dawo da zababben shugaban kasar.