✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kafa wa mai ciki kusa a kanta don ta haifi da namiji

Lokacin da ta isa asibitin, ta yi ta kokarin cire kusar daga kanta, amma ta kasa.

Wani mai ba da magani da wadansu suka yi imanin cewa, yana warkar da ciwo a Pakistan ya shawo kan wata mai juna biyu cewa za ta haifi da namiji idan ya kafa mata kusa a kokon kanta.

Likitoci a asibitin Lady Reading da ke Peshawar wani babban birni a kasar sun yi matukar kaduwa lokacin da suka dub mai juna biyun da ta yi ikirarin cewa, an kafa mata kusa mai tsawon inci biyu a kanta.

Hoton jikin dan Adam na D-ray ya tabbatar da ikirarin matar, kuma labarinta ne ya sa ma’aikatan asibitin suka yi shiru.

Matar ta ce, kusar da ke kanta wani ba da magani ne ya ba ta shawarar haka, cewa za ta haifi dan fari namiji maimakon ’yarta ta hudu.

Matar da aka sakaya sunanta, ta kasance “sane da abin da ke kanta, kuma tana cikin matsanancin jin zafi.”

Lokacin da ta isa asibitin, ta yi ta kokarin cire kusar daga kanta, amma ta kasa.

Ta shaida wa likitocin cewa, mijinta ya yi barazanar zai gudu ya bar ta idan ta haifi ’ya mace, don haka ta yi fatar samun namiji.

Wata makwabciyarta ce ta ba ta shawarar zuwa wajen mai maganin don samun biyan bukata.

Da farko matar ta shaida wa likitoci cewa, mai maganin ya umarce ta da ta rera wasu wakoki yayin da ya dauki doguwar kusa ya kafa mata a kai, amma bayan da suka duba raunin, sai likitoci suka tabbatar da cewa ba za ta iya yin wannan aikin da kanta ba, kuma wani ne ya yi.

Ba a san wanda ya yi aikin ba, amma a bayyane yake cewa matar ta amince da yin hakan.

Ta ce “Wata mata a unguwarsu ta yi irin haka kuma ta haifi namiji duk da cewa, na’urar duban dan tayi ta nuna jaririya ce a cikinta.”

Dokta Haider Suleiman Khan, likita a asibitin Lady Reading, ya shaida wa kafar labarai ta Dawn cewa matar “Tana da cikin wata uku kuma saboda tsoron mijinta ta je wajen mai maganin da ta yi imani da shi wanda ya ba ta laya da abubuwan da za ta karanta da kuma kafa mata kusar.”

’Yan uwan matar sun ji ihunta lokacin da ta ji zafin raunin kuma suka yi kokarin taimaka mata wajen cire kusar, amma ba su yi nasara ba.

Bayan gwajin hoton na’urar D-ray don tabbatar da cewa kusar bata shiga can cikin kwakwalwarta ba, likitoci sun yi nasarar cire ta daga kanta.

Maimakon sanar da ’yan sanda, sai likitocin suka wallafa hoton D-ray da kuma wannan labari mai ban al’ajabi a Intanet, inda cikin sauri ya fara yaduwa.

Daga karshe ’yan sandan Peshawar sun fara gudanar da bincike, kuma suna kokarin gano wanda ya kafa wa matar kusar don gurfanar da shi a gaban kotu.

“An kaddamar da rukunin musamman domin gurfanar da mai maganin bogin wanda ya yi wasa da rayuwar matar, sannan ya kafa mata kusa a kai, tare da alkawarin karya na haihuwar da namiji,” inji ’yan sanda.

Shugaban ’yan sandan Peshawar Abbas Ahsan ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, “Rundunar za ta binciki dalilin da ya sa likitan da ke jinyar bai kai rahoton lamarin ga ’yan sanda ba.”