✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 450 a Pakistan

’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan.

’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran.

Wani babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450.

Sai dai kuma shafin jaridar rnz na intanet ya ruwaito cewa, daga bisani an kubutar da akalla fasinjoji 100 yayin da ajali ya katse hanzarin wasu uku a yayin harin da ya auku a kudu maso gabashin Balochistan.

Kungiyar Baloch Liberation Army (BLA) mai yunkurin neman cin gashin kan yankin Balochistan, ta dauki alhakin garkuwar baya ga zargin hukumomi da mamaye arzikin yankin.

Kungiyar dai BLA ta dade ta na tayar da zaune tsaye a Pakistan kuma ta na ikirarin a bar mata yankunanta don rike madafun iko.