Wani dan asalin Jihar Taraba mazaunin Jihar Edo, ya zare wuka mai kaifi daga kugunsa ya dabata a cikinsa ya farke, inda a nan take sai ga hanjinsa ya fito waje.
Sai dai duk da haka, taurin zuciya bai sa ya ya da wukar ba yana kokarin ya kara soka ta cikinsa, yana rike da ita mutane suka zo suka taru a kansa, da kyar suka samu suka kwace wukar daga hannunsa.
- Ya kamata gwamnati ta kara kaimi kan matsalar tsaro – Rarara
- Sojojin Isra’ila sun kashe Bafalasdine, sun jikkata wasu mutum 13
Mutumin, mai suna Muhammadu mai kimanin shekara 40, dan asalin Jihar Taraba wanda ya ce, ya fito ne daga garin Nguroje da ke Gembu a Jihar.
Amma a cikin ikon Allah burinsa bai cika ba, domin bai mutu ba a lokacin har aka dauke shi aka kaishi wani asibiti mai zaman kansa daura da Babbar Kasuwar Shanu inda ya aikata wannan haukar.
A cewar wadanda suka dauke shi zuwa asibiti sun ce, yana gardama da cewa ba za a yi masa dinki ba, don haka ya fi son a barshi ya mutu.
Aminiya ta samu ganinsa kafin a garzaya da shi asibiti kuma ta yi masa
wasu tambayoyi in da ya amsa da
cewa, dalilin da ya sa ya dauki wannan
mataki, ita ce talauci ne ya yi masa katutu, don haka ne ya sa ya gwammace ya kashe kansa domin ya huta da wahala.
Shugaban ofishin ’yan sandan na yankin, D.O Ismaila, mai kula da yankin da Aminiya ta tuntube shi a kan matakin
da Muhammadu ya dauka, ko jami’an
’yan sanda sun samu wannan labarin? sai ya ce, lallai muna da labarin hakan.
Amma ya ce suna bincike a kansa sai sun gama kafin su bayyana komai.