’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da sau ɗaya a ɗakinsa.
Wakil ya ce a yayin bincike magidancin ya amsa cewa ya sha zakke wa ’yar tasa a gida, kuma bayan an yi mata gwaji a asibiti aka tabbatar cewa tana ɗauke da ciki wata uku.
Ya ce yarinyar ta shaida wa masu bincike cewa a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa garin iyayenta a Ƙaramar Hukumar Ningi da ke jihar ne mahaifin nata ya yi amfani da damar ya riƙa lalata da ita.
- An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi
- Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi
- ’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a Katsina
Bayan dawowar mahaifiyar ce ta lura da alamun juna biyu a tare da ’yar, kuma bayan ta titsiye ta, ta shaida mata cewa mahaifinta ne ya yi mata cikin.
Wakil ya ce rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.