✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya kashe mutum kan N200 a Yobe

Ana zargin dan sandan da hallaka mamacin ne saboda ya ki ba shi cin hancin Naira 200 da ya nema.

Wani Insfektan ’yan sanda ya caka wa mutum wuka har lahira kan cin hancin Naira 200 a garin Damaturu, fadar Jihar Yobe.

Ana zargin dan sandan da hallaka wani wanda ake zargin dillalin kwayoyi ne saboda ya ki ba shi cin hancin Naira 200 da ya nema.

Lamarin ya faru ne a Unguwar CMC, Zango, Damaturu, inda sufeto Mohammed Bulama, da marigayin suka fafata ranar Lahadi da karfe 5:05 na yamma.

Wata majiya ta ce “Sufeto Mohammed Bulama ya bukaci N200 daga hannun mamacin.

“Da mamcin ya ki amincewa, sai Insifeto Bulama ya kai masa hari da wuka, inda ya yanke masa wuya da kirji har ya kai ga mutuwarsa.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce kwamishinan runduanr, Garba Ahmed ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.

Da yake karin haske game da lamarin, jami’in ya ce takaddamar kan wani ciniki “ya rikide zuwa fada, lamarin da ya sa Bulama ya daba wa Dauda wuka a kirji, shi ma Bulama ya samu rauni a kai.

“Ba tare da bata lokaci ba an kama wanda ake zargin a hedikwatar ’yan sanda ta ‘C’ Dibision inda ya nemi mafaka.

“Sashen binciken manyan laifuka (CID) ta fara gudanar da bincike kuma a halin yanzu Bulama yana tsare a hannun har sai an gurfanar da shi a gaban kotu.” Inji shi.