✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos

’Yan sara-suka sun caccaka wa wani matashi dan shekara 23 wuka a wuya da kirji har lahira a yayin da yake hanyarsa ta zuwa shagonsa…

Gungun ’yan daba da aka fi sani da ’yan sara-suka yin caccaka wa wani tela dan shekara 23 wuka har lahira a garin Jos, Jihar Filato.

’Yan uwan matashin mai suna Aminu Abdullahi, sun shaida wa wakilinmu cewa ’yan sara-sukan sun caccaka masa wuka a wuya da kirji har lahira ne a yayin da yake hanyarsa ta zuwa shagonsa a unguwar Dutse uku.

Sun bayyana cewa an garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya riga ya yi halinsa, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar a yankin.

Wani yayan mamacin mai suna Abdulrahman Abdullahi, ya bayyana cewa: “Da farko wani dan sara-suka ne ya kwace wayar wani karamin yaro, kuma kanin nawa Aminu ya gani wanda ya yi kwacen shi ne ya je ya karbo wayar ya mayar wa mai ita, wanda hakan bai yi wa sauran Aminu ’yan sara-sukan dadi ba.

“Bayan sa’o’i da faruwar abun shi ne suka zo suna barazanar kashe shi saboda abin da ya yi wa abokinsu, to da ya ga haka sai ya yi sauri ya sanar da ofishin ’yan banga mafi kusa domin su dauki mataki.

“Bayan ya kai kara yana hanyar dawowa zuwa shagonsa ne gungun ’yan sara-sukan suka taru suka soka masa wuka a kirjinsa da wuyansa.

“Ya yi nasarar kama daya daga cikinsu, har ’yan banga suka zo suka tsare shi. Amma kafin a ba shi wata kulawar asibiti rai ya riga ya yi halinsa,” in ji Abdulrahman.

Mahaifinsu Malam Abdullahi and Hannatu Suleiman, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin hukunta duk mai hannu a cikin lamarin domin ya zama darasi ga saura.

Wakilinmu ya samu bayani cewa an tsare karin mutum biyu daga cikin bata-garin da suka yi aika-aikan.