Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama wani dan shekaru 24 bisa zargin kashe Lawan Adamu, mai shekaru 28 a Unguwar Nayi-Nawa cikin garin Damaturu, babban birnin jihar.
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim ya ce, “A ranar 15 ga Satumba, ‘A’ Division Damaturu ta samu kiran waya kan gawar da aka tsinta.
“Nan take jami’anta suka isa wurin suka gano wanda abin ya shafa da yanka a makogwaro da raunuka masu yawa; kuma sun kuma gano wuka mai dauke da jini a wurin a jefe.
“An kai gawar zuwa babban asibitin Damaturu, inda wani likita ya tabbatar da rasuwar sa sai aka ajiye gawar a dakin ajiyar gawa na asibiti.”
- Aminu Dantata ya ba mutanen Maiduguri tallafin N1.5bn
- Biliyan N250 Matawalle ya wawushe a Zamfara —Gwamna Lawal
- ’Yan tawaye sun kai hari makarantar horas da jami’an tsaro a Mali
A cewarsa, “wanda ake zargi da aikata wannan aika-aika a kan hanyar unguwar Nayi-Nawa ya kama marigayin da kokawa sanadiyar takaddama tsakaninsu, daga bisani ya daba masa wuka a wuyansa ya jefar da shi nan ta ke a mace.
“Kwamishinan ’yan sandan jihar Yobe, Garba Ahmed, ya ba da umurni a fadada binciken domin gano musabbabin faruwar lamarin.
“Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a gaggauta gudanar da bincike, domin kuwa tabbas za a yi adalci.