Jami’an tsaro sun cafke wani matashi mai shekaru 30 da ya sare hannuwan mahaifiyarsa da adda saboda rashin jituwa.
Shaidu sun ce matashin ya kuma yi wa mahafiyar tasa mai shekaru 65 mummunan sara a kanta, sannan ya yayyanke ta a kafarta da wasu sassan jikinta.
- Kotu ta dawo wa dan majalisar NNPP kujerarsa a Kano
- Gwamnatin Tinubu za ta binciki yadda Buhari ya tafiyar da shirin N-Power
Wanda ake zargin ya yi wa datijuwar wannan aika-aika ne a kauyne Akibo da ke Karamar Hukumar Obafemi Owode ta Jihar Ogun.
A cikin daren ranar Laraba ne aka ji hayaniya a gidan tsohuwar, inda makwabta suka je domin kai dauki, amma ko da suka isa, sai suka same ta cikin jini, da hannuwanta biyu duk an datse su, da kuma sara a kanta, shi kuma dan nata yana tsaye a kanta ya rike wata sharbebiyar adda.
Jaridar Punch ta ruwaito wani makwabcinsu yana cewa wanda ake zargin ya kuma sari mahaifiyar tasa a kafa da wasu sassan jikkinta, amma an kai ita asibiti domin ba ta kulawa.
PUNCH Metro ta ruwaito kakakin yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, na tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rundunarsu ta cafke matashin kuma rundunar na gudanar bincike kan lamarin.