’Yan sanda sun fara farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya yi wa matarsa kisan gilla da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel.
“Ya aikata hakan ga matarsa ’yar shekaru 40 ta hayar amfani da adda, inda ya kashe ta ya kuma tsere saboda wasu dalilai da har yanzu ba a tantance ba,” in ji sanarwar.
Tuni dai ’yan sanda suka fara kokarin cafke wanda ake zargin do ya fuskanci shari’a.
- Jami’an tsaro sun hana taron kwamitin amintattun PDP
- Abin da jama’a ke cewa game rayuwar Aminu Dantata
A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutane biyu da kasa zargin sun kashe wani mutum bisa zargin satar waya a garin Ngalda da ke Ƙaramar Hukumar Fika.
“An zarge su ne da laifin kashe wani bisa zargin da da satar wayar hannu da na’urar cajin waya, kima dukkansu sun amince da aikata laifin kuma suna fuskantar bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya bukaci mazauna yankin da su nemi hanyoyin warware rigingimu cikin lumana, su guji daukar doka a hannunsu.