Wani maraya ɗan shekara 15 yana kwance cikin mawuyacin bayan sara da adda da karaya bakwai da yake zargin dagacinsu ya yi masa a yankin Kagarawal da ke Jihar Gombe.
Adamu Muhammad na zargin cewa a ranar 5 ga watan Disamba, 2024 ne dagacin nasu, Alhaji Bello A. Usman, ya ɗauki doka a hannunsa, ya sassare shi sannan ya ba da umarni aka jefar da shi a bola.
Hakan ta faru ne bayan basaraken ya zargi Muhammad da yin sata a gidansa da tsakar dare.
A kan wannan dambarwa ne wakilin Aminiya ya ziyarci yankin Kagarawal domin jin haƙiƙanin abin da ya faru, inda ya zanta da Muhammad da ke kwance yana jinya da kuma dagacin da sauran jama’a, ko da yake yawancin waɗanda akae nemi magana da su sun yi guma da bakinsu.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin yin magana da ’yan unguwar amma suka nemi mu shafa musu ruwan sanyi.
‘Ya yi min karaya bakwai da adda’
Adamu, wanda ke kwance yana jinya ce, ranar wata Laraba ce ya yi faɗa da wata ’yar maƙwabtansu, har ya mare ta, ita kuma ta kai ƙararsa wajen ’yan banga, shi kuma saboda gudun faɗan da mahaifiyarsa za ta yi masa ya ƙi komawa gida.
A cewarsa, “har dare ya fara ban samu wajen kwanciya ba, sai na tafi gidan dagaci na kwanta a gindin wata bishiya a kan da safe zan roƙa a je a ba ta haƙuri. Ina kwance da misalin ƙarfe 11 sai dagaci ya fito ya yi mini ihun ɓarawo.
“Na tashi zan tsere, sai ya tare ni ya kama ni ya kira matarsa ta kawo masa adda, ya sa suka danne ni ya dinga sassara ni, ya ji mini ciwo ya kuma sa aka kai ni bola a daren a jefar, ko da zan mutu, wai ba’a gidansa ba.”
Adamu ya ce yana kwance a kan bola ba zai iya tashi ba saboda karaya da ke a jikinsa, “can zuwa wani lokaci sai na ji ƙarar babur, shi ne na yi ƙara sai mutumin ya tsaya.
“Yana zuwa sai na ga ɗan banga da aka kai ni ƙara wajensu ne, ya san shi. A nan ne yake tambaya ta me ya faru, sai na gaya masa. Muna magana, sai ga motar ’yan sanda ta zo wucewa sai ya yi musu magana suka ɗauke ni zuwa ofishinsu na Gombe Division, daga nan suka tafi da ni Asibitin Gwamnati Tarayya.”
Asibiti na neman N500,000
Ya ce asibitin ne aka yi masa ɗinki a inda ya ji ciwon, “aka wanke ƙasar da take ciki, amma ba a ɗaura karaya ko ɗaya ba, sai mun ajiye Naira dubu dari biyar kafin a fara masa jinya.”
Game da yawan raunin da ke jikinsa, saurayin ya ce, “Da farko ban sani ba domin ko’ina a jikina akwai sara, har babbar yatsata ta kusa guntulewa, fata ce ta riƙe ta. Ya tsinka min agara, ya ji min ciwo a kunne, amma dai yanzu an tabbatar min karaya bakwai ne a jikina.”
Ya hana a yi mini ɗori
Saurayin ya ƙara da cewa wata mata mai ɗori ta so ta taimaka ta ɗaura shi, amma wanda ake zargin ya yi mata barazanar cewa idan ta kuskura ta ɗora shi zai saɓa mata.
“Haka aka ɗauko ni daga gidanta da aka kai ni, aka dawo da ni gida, inda a tsawon kwana 10 ko sau daya ba a wanke ciwon ba har ya fara wari,” in ji shi.
Ya roƙi al’umma da su duba maraicinsa a kawo masa ɗauki domin ko abincin da za su ci a gidansu ba sa samu, suna iya kwana uku ba a ɗora sanwa ba.
Adamu ya roƙi gwamnati da ta shigo lamarin don a ceto rayuwarsa ganin halin da yake ciki, “ga har yanzu shi dagacin bai haƙura ba, yana mana barazanar cewa ko nan da yaushe ne idan na warke sai sun yi shari’a, bayan ga halin da nake ciki na jinya da rashin gata.
“Da wanne zan ji, so yake mamata ta mutu saboda takaici?”
‘Ban taɓa yin sata ba’
Game da zargin sata, Adamu ya ce “Gaskiya ni ba ɓarawo ba ne, ban taɓa sata ba, hukuma ma ba ta taɓa kama ni ba, shi ya sa da yarinyar ta kai ni wajen ’yan banga na gudu, saboda ban san ya zanyi ba, ni latirisha ne a gareji kusa da Masallacin Idin Sarki.”
Ya ce, bayan abokiyar faɗansa ta kai shi wajen ’yan banga suka ce kuɗin marinta Naira dubu shida ne kuma ba zai iya biya ba, “idan kuma na koma gida mahaifiyata za ta yi min faɗa shi ne na ji tsoro, dalilin ke nan da na je gidan Dagaci ya kwanta.”
A bi mana haƙƙinmu —Mahaifiyar Adamu
Mahaifiyar saurayin, Malama Yelwa Muhammad, ta ce, ba su san shi da sata ba, “ƙaddara ce, shi ya sa a garin guje wa fushina ya je gidan Dagaci don ya kwana.
“Da ya yi haƙuri da irin faɗan da zan yi masa da haka bai faru ba, domin duk faɗan da zan yi masa babu yadda za a yi na illata ɗana haka.
“Ni dai ba ni da abin da zan iya faɗi illa na yi kira ga gwamnati da ta bi kadun yaro, domin maraye ne ba shi da uba kuma shi ne mai ɗan nemo mana abin da za mu ci, idan ya fita aikinsa na gareji, sai gashi an tsugunar mana da shi,” tana mai cewa ba taɓa sanin yaron da sata ba.
Mara lafiya ya fara wari
Malama Yelwa ta ce mai ɗorin ta gaya mata cewa dagacin ya taɓa kawo mata ƙaninsa da ɗan maƙwabta ta ɗora su, amma kuma ba ta san me ya sa ya hana ta ta ɗora Adamu ba.
Ta ce saboda ba su da ƙarfi, tunda abin ya faru haka suke kwana da yunwa sai ranar da Allah Ya sa makwabta suka waiwaye su, “ko idan ’yan garejinsu sun samu ɗan wani abu su saya masa lemon kwalba.
“Ranar da ba su samu ba haka yake haƙura, yana jinyar ma yana kwana bai ci ba, ga shi nan a kwance a ɗaki ba kula har ya fara wari.”
Yadda muka ga Adamu —’Yar uwarsa
Yayar Adamu mai suna Ummi Muhammad, ta bayyana cewa ƙanin nata bai taɓa kaiwa dare bai dawo gida ba, sai a ranar da abin ya faru.
Ummi ta ce ranar sun kai har ƙarfe 11 na dare suna jira bai dawo, sai ita da ƙaninta Suleiman suka fita neman sa amma ba su gan shi ba, dole suka haƙura suka dawo suka ba wa mahaifiyarsu haƙuri cewa ta bari zuwa wayewar gari.
Can da misalin ƙarfe 12 saura, a cewarta, sai suka ji motar ’yan sanda a ta tsaya a gaban gidansu, ana buga ƙofarsu, sai ta tambaya, suka ce su buɗe ’yan sanda ne.
Ummi ta ce har mahaifiyarsu ta ƙi yarda su buɗe sai ita ta ce mata ta gane muryar ɗaya daga cikinsu sai suka buɗe kofa, da ta tambaye su me ya faru “sai ya ce ba mamiji ne a gidan?” Ta ce akwai.
Sai ta taso Suleiman ya bi su ita kuma tana bin su da ƙafa, suna shiga wata kwana sai ta ga Adamu kwance cikin jini, jikinsa da sara da karaya, “sai fata ce ta riƙe wani wajen, ƙafar tana lilo ta karye har agarar ƙafarsa ta yanke, a layin gaba da gidan Dagaci inda suka jefar da shi.”
Ta ce “daga nan sai asibiti aka kuma ƙi yi masa jinya inda aka ce sai sun ajiye Naira dubu dari biyar sannan a fara masa jinya.”
Mun sanar da hukuma — Lauya
Wani lauyan mai zaman kansa da ya tsaya don bin kadun Adamu, Barista Sa’idu Mu’azu Kumo, ya ce sun rubuta wa Kwamishinan ’Yan Sanda da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya da Sakataren Gwamnatin Jihar da Mai Martaba Sarkin Gombe da hukumomin tsaro don ganin an gaggauta gurfanar da Dagacin a gaban ƙuliya.
Barista Sa’idu Kumo ya ce rahoton aika-aikar da kuma barazanar da ake wa iyayen yaron ne ya sa ya shiga lamarin don tsaya musu tunda maraya ne mara gata, ga kuma karaya har bakwai a jikinsa, har kwanaki kusan goma ya yi ba a ɗora shi ba kuma yana aman jini.
Ya ce ko da sata yaron ya yi aka kama shi, hukuncinsa a dokar ƙasa tara ce ko zaman gidan yari na shekara ɗaya, ba ɗaukar doka a hannu a sassare shi ba.
Lauyan ya ce “bai kamata a ce dagaci da ke wakiltar al’umma ya aikata irin wannan ta’asa ba, kuma har ya dinga barazanar cewa da ma kashe yaron ya yi niyyar yi sannan a zuba ido a bar shi.”
Ina ƙoƙarin kare kaina ne —Dagaci
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Dagacin Kagarawal, Alhaji Usman A. Bello, game da zargin, inda ya musanta cewa ya sassari yaron.
Ya bayyana cewa an jima ana yi musu sata kuma yana raba dare bai yi barci ba.
“A ranar Laraba 5 ga watan Disamba 2024 ina zaune da misalin ƙarfe 2:35 na dare na ji motsin mutum yana ƙoƙarin sace mana sitabileza, sai na yi wuf na fito, na ga mutum na ce kai, sai ya nemi guduwa, inda a nan ne muka fara artabu da shi har na ƙwace wukar da ke hannun yaron, na sare shi sau ɗaya a lokacin,” ji shi.
A cewarsa, yaron ne ya fara saran sa da wuka a ƙafa, ya ji ciwo, amma shi a sanin sa sau ɗaya ya sari yaron, a ƙoƙarinsa na kare kansa.
Ya kuma ƙaryata cewa ya ba da umarnin a jefar da Adamu a bola, amma bai sani ba ko bayan kai shi asibiti ba ne wasu suka sassara shi suka kai shi bola.
Muna bincike —’Yan sanda
Da wakilinmu ya tuntuɓi DPO na Gombe Division ya buƙaci mu tuntubi hedikwatar runduar ta jihar.
Wakilinmu ya tuntuɓi kakakin ’yan sanda na jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, wanda ya shaida wa masa cewa rundunar ta samu rahoton al’amarin daga Gombe Division, amma an miƙa rahoton zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin zurfara bincike.
Jami’in ya bayyana cewa da zarar sun kammala nasu bincike zai sanar da inda aka kwana kan lamarin.