✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace gwamnati ta magance matsalar tsadar kayayyaki – Alhaji Iliyasu

Shugaban kungiyar Masu sayar da Buhuna ta Jihar Filato ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance matsalar tsadar kayan masarufi da ake fama…

Shugaban kungiyar Masu sayar da Buhuna ta Jihar Filato ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance matsalar tsadar kayan masarufi da ake fama da shi a yanzu kasar nan.
Shugaban Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a Jos.
Ya ce sakamakon wannan matsala ta tsadar kayan masarufi, “yanzu harkokin kasuwanci sun shiga cikin wani mawuyacin hali a Najeriya  ‘yan kasuwa  manyan  da kanana  kowa dabararsa ta kusa karewa.”
Ya ce “gaskiyar magana a kasar nan kashi 95 cikin 100 na kayan da muke rayuwa da su kamar abinci da sutura ana shigo da su ne daga kasashen waje. Kuma dukkan wadannan kayayyaki da ake sayowa daga kasashen waje da Dalar Amurka ake amfani wajen sayo su. Sai ya zaman to Dalar nan ba ta samuwa, rashin samuwar Dalar ne ya kawo mana wannan halin kunci na tsadar kayayyaki da muke fama da shi a Najeriya.”
Ya ce duk da mun san gwamnati tana yin wannan abin ne da nufin gyara, ya kamata gwamnatin ta taimaka kan wannan hali da ake ciki.
Ya bai wa gwamnati shawara, inda ya ce gwamnati ta zabo kamfanoni da ‘yan kasuwa nagari masu sarrafa kayayyaki ta ci gaba da canza masu da Dalar nan, don suje su rika sayo kayayyakin da ake bukata a kasar nan.
Har ila yau, ya ce yakamata ta dauki mataki kan kamfanoni da ‘yan kasuwar da take canzarwa da Dala, amma  ba sa sayo kayayyakin da suke cewa za su sayo a  kasashen ketare.
A karshe ya yi kira ga ‘yan kasuwa kan su koma ga Allah a yi ta addu’o’i Allah don samun mafita.