Wata dattijuwa mai shekaru 51 ta maka makwabcinta a kotu, bisa zargin kwashe mata rufin gida.
Kotun da ke zamanta Abuja dai na tuhumar mutumin ne da laifin keta, duk da ya musanta zargin.
- ’Yan bindiga sun harbe jami’an tsaro 12 a Kaduna
- Ganduje zai tantance jam’iyyu kafin kamfe a filin wasa na Sani Abacha
Dan Sanda mai gabatar da kara Mista Stanley Nwafoaku ya bayyana wa kotun cewa matar, “Ta bayyana mana cewa cacar baki ce suka yi, shi kuma ya yi amfani da wannan damar ya kwashe mata rufin gida, sannan ya lalata mata kwatami.”
A cewarsa, dattijuwar ta shigar da korafin ofishinsu da ke unguwar Jabi ne ranar 1 ga watan Disamba.
A cewar dan sandan laifin ya sabwa sashi na 327 na kundin Penal Code.
Alkalin kotun Muhammad Wakili ya bai wa wanda ake zargi beli kan N500,000, bisa sharadin kawo mai tsaya masa da ya mallaki takardar shaidar zama dan kasa, da lambar tsaro ta banki, hadi da hoton fasfo.
Daga nan ne kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu.