An sake ɗauke wuta gaba ɗaya a babbar tashar lantarki ta Nijeriya.
Babbar tashar wutar lantarkin ƙasar ta gaba ɗaya ne da misalin karfe 12 na ranar Alhamis, lamarin da ya haddasa katsewar wuta a duk layukan rarraba wutar a fadin Nijeriya.
Kimanin kwana biyu ke nan bayan irin haka ta faru a ƙasar, duk a cikin watan nan na Nuwamba.
Wannan shi ne karo na 10 da wutar lantarki ta ɗauke a faɗin Najeriya sakamakon lalacewar babbar layin lantarkin ƙasar a cikin wannan shekara ta 2024.
Zuwa lokacin da muka kammala wannan labari dai Kamfanin Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (TCN) ba ta bayyana musabbabin matsalar ba.
Amma Kamfanin Rarraba Lantarki na Jos, ya tabbatar cewa wutar da yake samu daga babban layin lantarki na ƙasa ya ɗauke gaba ɗaya.
Kamfanin ya ce, “muna da ran komai zai dawo yadda yake da zarar an shawo kan matsalar.”