Wutar lantarkin Najeriya ta sake daukewa gaba daya tun daga tushe a ranar Litinin, lamarin da ya jefa ilahirin kasar cikin duhu.
Lamarin na zuwa ne watanni bayan Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta kaddamar da wani shiri na musamman domin inganta wutar lantarki a kasar.
- Poland za ta ba ’yan kasa horon Soji
- Na yi mamakin yadda Isra’ila ta hana mu makaman yakar Rasha – Shugaban Ukraine
Wannan daukewar, wacce ita ce ta bakwai a cikin shekarar nan, ta faru ne da misalin karfe 10:51 na ranar Litinin din nan.
Da misalin karfe 12:00 na rana ne dai, bayanai daga Kamfanin Samar da Lantarki na Najeriya (TCN) sun nuna cewa, adadin wutar ya yi kasa daga sama da megawat 3,712 da ake da shi a dukkan manyan layukan samar da wutar lantarkin kasar guda 21.
Sai dai Kamfanin ya ce adadin wutar lantarki ya ci gaba da raguwa cikin tazarar sa’a guda kuma daga bisani ta dauke gaba daya.
Ya zuwa yanzu dai, Kamfanin na TCN bai kai ga bayyana makasudin daukewar wutar ba, sai dai wasu majiyoyi na cewa hakan ba zai rasa nasaba da kokarin inganta babban layin samar da wutar na Jos da Bauchi da za a soma a Litinin din ba.
Tuni dai wasu daga cikin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki da suka hada da na Enugu, Kaduna da kuma Kano suka fitar da sanarwar ankarar da abokan huldarsu halin da ake ciki.
A kwanaki kalilan da suka gabata ne dai masu amfani da lantarki suk ce sun ga ingantuwar samun lantarki a baya-bayan nan.
Tun cikin watan Yulin bana, masu amfani da lantarki sun ce an samu karin samar da lantarki a bangarori daban-daban.