Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya A’isha Buhari ta caccaki Mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu, inda ta ce yana shiga gonarta wajen wuce gona da iri a aikinsa.
Haka kuma A’isha Buhari ta sake tabo Mamman Daura, inda ta ce Garba Shehu ya raba hankalinsa, inda yake karbar umarni daga Mamman Daura maimakon wanda ya dauke shi aiki.
A’isha Buhari ta bayyana haka ne a wani sako da ta sanya wa hannu, sannan mai taimaka mata kan harkokin watsa labarai Suleiman Haruna ya raba wa manema labarai, inda ta nuna yadda mai magana da yawun mijin nata ke wuce gona da iri wajen gudanar da aikinsa.
Hajiya A’isha Buhari ta nuna takaici kan yadda ta ce Garba Shehu na kware wa Shugaba Buhari baya, saboda yana raba hankalinsu wajen aiki, inda yake karbar umarni daga wadansu mutane na daban.
Ta kuma koka kan yadda wani lokaci akan samu abin magana da ke shafarta da kuma Shugaba Buhari, har a yi ta yayatawa a duniya, amma Garba Shehu ba ya tsayawa ya kare martabarsu a lokacin da bukatar haka ta taso.
Hajiya A’isha Buhari ta kara da cewa Garba Shehu ya taba cewa ofishin Uwargidan Shugaba Kasa ba zai yi aiki ba, kuma ya shaida wa wadansu na kusa da shi cewa Mamman Daura ne ya sa shi ya fadi haka.
Ta ce a wuraren da aka san abin da ya dace, kamata ya yi Garba Shehu ya ajiye aikinsa.
Uwargidan Shugaban Kasar ta kara da zargin cewa Garba Shehu ya fi karkata ga wadansu mutane na daban, inda ta bayyana mutanen a matsayin masu ikon- boye a Fadar Shugaban Kasar duk da cewa ba zababbu ba ne.
Ta yi misali da dambarawar da aka yi a Fadar Shugaban Kasar, wadda aka yada a wani faifan bidiyo, inda a ciki take kumfar baki cewa an rufe mata kofar wani gida da ke fadar, tana neman mutanen da ke ciki, wadanda ta tabbatar da cewa iyalan Mamman Daura ne kan su bude mata kofa.
A’isha Buhari ta ce an yi ta yin maganganu a kan labarin amma Garba Shehu bai fito ya bayyana asalin yadda lamarin yake ba.
Duk da cewa ba ta fito fili ta ambaci maganar auren da aka yi ta yayatawa ta Intanet ba cewa Shugaba Buhari zai auri wata minista, Uwargidan Shugaban Kasar ta ce Garba Shehu bai yi komai ba wajen kashe maganar ko fayyace gaskiyar al`amarin, duk da cewa aikinsa ne kare martabar Fadar Shugaban Kasa.
‘Garba Shehu ba zai yi cacar baki da Uwargidan Shugaban Kasa ba’
Wani na kusa da Garba Shehu da Aminiya ta tuntuba ya ce Garba Shehu ba zai yi cacar baki da Uwargidan Shugaban Kasa ba.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda rikici ya shiga tsakanin Uwargidan Shugaban Kasa da iyalan Mamman Daura a watan Oktoba bayan dawowarta daga tafiya inda ta kwashe kusan wata biyu ba ta kasar nan. Bayan dawowarta ce wani faifan bidiyo ya bayyana, wanda ya kara fito da rikicin da ke gidan fili.
Wannan ya nuna ba Shugaba Buhari ke mulki ba – PDP
Da Aminiya ta tuntubi Jam’iyyar PDP kan lamarin da ke faruwa, jam’iyyar ta ce wannan lamarin ya kara tabbatar da cewa Shugaba Buhari bai cancanci zama Shugaban Kasa ba, kuma hakan ya sa ya kasa tafiyar da harkokin mulki.
Wannan bayani ya fito ne daga Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP, Kola Olonbondiyan, inda ya ce bayanin A’isha Buhari cewa wadansu mutane suna bayar da umarni a madadin Shugaban Kasa ba tare da saninsa ba, ya nuna cewa wadansu ne suke yin mulki.
Daga nan sai PDP ta shawarci Shugaba Buhari ya gyara gidansa domin ya daina jefa kasar nan cikin abin kunya.