✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WTO: Buhari na ganawar sirri da Okonjo-Iweala

Tsohowar Ministar Kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, mai takarar shugaban Hukumar Kasuwanci ta Duniya na ganawa da Shugaba Buhari

Shugaba Buhari na ganawar sirri ta tsohowar Ministar Kudi da Tattalin Arziki, Ngozi Okonjo-Iweala, wadda ke takarar shugabancin Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Buhari ya bayyana goyon bayansa ga Okonjo-Iweala, wanda a yanzu ta kai matakin karshe na zaben tsakaninta da abokiyar hamayyarta, Yoo Myung- hee, ‘yar kasar Koriya ta Kudu.

Minista a Ma’aikatar Masana’antu, Maryam Katagum, wadda ita ke shugabantar yakin neman zaben Okonjo-Iweala ta kwatanta ta da “wadda ta fi cancanta ta jagoranci WTO”, kamar yadda ta fitar a takardar da ta raba wa ’yan jarida a Abuja.

Okonjo-Iweala ta isa Fadar Shugaban Kasar ne tare da Ministan a Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Zubair Dada; Ministan Masana’antu, Niyi Adebayo; da kuma Minista a Ma’aikatar Masana’antu, Maryam Katagum.

Katagum ta kuma yaba wa kungiyoyin ECOWAS da EU da suka goyi bayan ’yar takarar ta Najeriya.