✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Willian zai tsawaita kwantaraginsa a Chelsea

dan kwallon tsakiya na kulob din Chelsea Willian, dan kasar Brazil, a ranar Talatar da ta wuce ya ba da sanarwar niyyarsa ta sabunta kwantaragin…

dan kwallon tsakiya na kulob din Chelsea Willian, dan kasar Brazil, a ranar Talatar da ta wuce ya ba da sanarwar niyyarsa ta sabunta kwantaragin shekara biyar da kulob din Chelsea.

Mai shekara 30, Willian a bara ya so ya bar kulob din Chelsea ganin ba ya ga-maciji da tsohon koci Antonio Conte.  Sai dai ganin kulob din ya yi sabon koci Maurizio Sarri daga kulob din Napoli ne ya sa dan kwallon ya canja shawarar zama a kulob din.

Tun bayan da Sarri ya karbi ragamar kulob din yake dasawa da Willian.  Sabon kocin ya nuna Willian yana daga cikin ’yan kwallon da yake ji da su a kulob din.

Willian ya ce wannan dalili ne ya sa ya canja shawara, kuma nan gaba kadan zai sabunta kwantaragi har na tsawon shekara 5.

Kwantaragin Willian za ta kare ne a shekarar 2020 amma yana sa ran sabuntawa zuwa 2025.  

A shekarar 2013 ce Willian ya canja sheka daga kulob din Anzhi Makhachkala da ke Rasha zuwa Chelsea kuma tun daga wancan lokaci ne tauraruwarsa take haskakawa.

Rade-radin da ake yi zai koma FC Barcelona na Sifen ko Manchester United na Ingila, yanzu ya sha ruwa.