✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wike ya kara yawan hadimansa zuwa mutum 200,000

Wike ya kara yawan hadiman nasa daga mutum 100,000 zuwa 200,000.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kara yawan wadanda suke yi masa hidima daga mutum 100,000 zuwa 200,000.

Wike da kansa ya bayyana haka a wajen bikin rantsar da runkunin farko na hadimai na musamman su 100,000 wanda ya gudana a mazabar Sanatan Ribas ta Gabas da ke Karamar Hukumar Ikwerre a ranar Juma’a.

Gwamnan ya bayyana cewa, sakonni mara adadi da yake samu daga ‘yan jihar dangane da neman mukamin ya sa ya nada hadimai da yawa.

Ya ce, jama’arsa na ganin ayyuka sun yi masa yawa don haka akwai bukatar ya ba su dama su taya shi gudanar da wasu harkokinsa.

Kazalika, ya ce da yawan ‘yan jihar sun amince su bayar da tasu gudunmawa ba tare da yanka musu albashi ba.

A cewarsa, hakan ce ta ga dacewar ya kara yawan hadiman nasa daga mutum 100,000 zuwa 200,000.

Gwamnan ya ce, ya umarci shugabannin siyasa na jihar kowa ya bincika a yankinsa sannan ya zabo masa wadanda ake ganin sun cancanta a bai wa mukamin.

(NAN)