Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da soma bincike kan wasu magungunan tari guda hudu da Kamfanin Maiden Pharmaceuticals ya yi a Indiya da ake zargi sun yi sanadiyar mutuwar yara 66 a kasar Gambiya.
WHO ta yi gargadin cewa, mai yiwuwa an rarraba gurbatattun magungunan a wajen kasar da ke yammacin Afirka, inda ake fargabar hakan ka iya yaduwa a duniya.
- Kamfanin Google Cloud zai bude ofishinsa na farko a Afirka
- Yadda aka horar da manoma sababbin dabarun noma a Gombe
Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manema labarai cewa akwai yiwuwar cewa maganin sanyi da tari guda hudu da ake magana a kai na da alaka da ciwon koda da kuma mutuwar yaran 66.
Tedros ya ce hukumar ta WHO tana kuma ci gaba da gudanar da bincike kan kamfanin tare da hukumomin da abun ya shafa a Indiya.
Dangane da faddakarwar samfuran magungunan da WHO ta bayar guda hudu sune, Promethazine Oral Solution, Kofexmalin Baby Cough Syrup, Makoff Baby Cough Syrup da Magrip N Cold Syrup.
Har ya zuwa yanzu, masana’antar da aka bayyana ba ta ba da cikakken bayani ga WHO kan aminci da ingancin wadannan magungunan ba.
Bincike daga dakin gwaje-gwaje na samfuran magungunan ya tabbatar da cewa sun kunshi gurbatattun sinadarin diethylene glycol da ethylene glycol da ya wuce kima.
Ko a watan da ya gabata sai da Ma’aikatar Lafiya ta Gambia ta bukaci asibitoci su daina amfani da maganin paracetamol na yara, har sai an kammala bincike, bayan da akalla yara 28 suka mutu sakamakon ciwon koda.