✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

WHO ta ba da izinin amfani da rigakafin COVID-19 da Indiya ta samar

Nau’in rigakafin na da sahihancin kashi 78 wajen yaki da cutar ta COVID-19.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ba da izinin fara amfani da nau’in rigakafin Coronavirus na Covaxin da Kamfanin Bharat Biotech na Indiya ya samar.

Hakan na zuwa ne bayan gwajinsa tare da gano tasirinsa a yaki da cutar wadda zuwa yanzu ta hallaka mutane fiye da miliyan biyar a sassan Duniya kamar yadda RFI ya ruwaito.

Hukumar WHO ta ce za a iya fara amfani da nau’in rigakafin na Covaxin samfurin India a yanayi na gaggawa don yaki da cutar ta covid-19 da ke ci gaba da kisa a sassan Duniya.

Nau’in rigakafin na Covaxin shi ne irinsa na farko da aka samar tare da yin gwajinsa cikin kasar India kuma WHO ta sahale amfani da shi inbanda sauran rigakafi da kamfanonin magani na kasar ke taya aikin samar da su.

A cewar hukumar, nau’in rigakafin na da sahihancin kashi 78 wajen yaki da cutar ta COVID-19 bayan gwajin allurarsa sau bibbiyu kan jama’a cikin makwanni 4 da suka gabata.

WHO ta bayyana cewa nau’in rigakafin na Covaxin zai yi tasiri hatta a kanana da matsakaitan kasashe la’akari da saukinsa wajen adanawa da kuma dadewar da ya ke gabanin lalacewa.

Nau’in rigakafin na India ya zama rigakafi na 8 da zuwa yanzu Duniya ke amfani da shi don yakar cutar bayan Pfizer da BioNTech da Moderna da AstraZeneca da Johnson and Johnson baya ga Sinopharm da Sinovac.