Hukumar Samar da Abinci ta Duniya (WFP), ta kashe kimanin Dala miliyan 95 wajen sayen kayan abinci da ake nomawa a Najeriya domin aikin tallafawa a yankin Arewa maso Gabas. Babban Daraktan Hukumar WFP, Mista Dabid Beasley ne ya bayyana haka lokacin da ziyaraci Maiduguri cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 7 ga Satumban nan. Mista Beasley ya ce hukumar ta kuma zuba Dala miliyan 212 a harkokin tattalin arzikin kasa ta hanyar musayar kudi da aka tsara domin samar da abinci da tallafin abinci mai gina jiki ga ’yan gudun hijira a yankin. Ya ce wannan adadi ya hada da kudin dakon kaya da albashin ma’aikata ’yan kasa da kuma sauran kudaden gudanar da ayyuka.
Mista Beasley ya yi gargadin cewa gaba dayan halin da ake ciki yana da matukar tayar da hankali, inda karancin abinci ya yi muni a wurare da dama a tsakanin watan Yuni da Satumba.
Ya ce, wasu daga cikin kalubalen da suke kawo cikas ga burin hukumar na isa lungunan yankin su ne rashin tsaro da munin hanyoyi da kuma rashin sako kaya daga tashar jiragen ruwa ta Legas. A cewarsa wadannan matsaloli suna kawo cikas ga hukumar wajen isa lunguna domin kai kayayyakin abinci masu gina jiki ga yara da iyalan da suka cancanta.
Shugaban na WFP, ya yaba wa gwamnatin Najeriya da kungiyoyin jin kai kan goyon baya da sadaukar da kai da suke yi wajen magance wahalhalun da jama’a suke ciki a yankin.
A lokacin ziyarar tasa, Mista Beasley ya gana Mataiamkin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Usman Durkwa da shugabannin jama’a da mata masu shayarwa a sansanin ’yan gudun hijira da ke sansanin masu yi wa kasa hidima da ke Maiduguri.