Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗaura wani sabon danba na inganta harkokin koyo da koyarwa, inda ta shirya wani gagarumin horo ga malaman jihar wanda Cibiyar Athena Centre for Policy and Leadership, tare da haɗin gwiwar Golden Links Educational Services, suka jagoranta.
A cewar sanarwa da kakakin Cibiyar Athena, Aliyu Jalal ya fitar, ya ce, “taron horon, wanda masana daga cikin gida da ƙasashen waje suka gudanar, ya horar da malamai 100 kan sabbin dabarun koyarwa da suka dace da ƙarni na 21 domin inganta koyo da koyarwa da tunani mai zurfi, da kuma hanyoyin amfani da dabarun ilimi na zamani domin samar da ilimi mai inaganci.”
- Mutum 20 sun mutu, 66 sun jikkata a harin da Isra’ila ta kai Lebanon
- Mun bai wa jami’anmu umarnin bincikar gwamnonin da ke kan mulki — EFCC
Shugaban Cibiyar tsare-tsare da gudanar da mulki ta Athena, Osita Chidoka, ya ce wannan nasara ce babba, inda ya yaba da hangen nesan Gwamna Dikko Umaru Radda na ɗaukar wannan matakin na inganta ilimi.
“Yadda Gwamnan Jihar Katsina ya amince a ƙaddamar da gwajin horon a jiharsa cikin sauri ya nuna yadda yake bai wa ɓangaren ilimi muhimmanci,” in ji Chidoka.
Kwamishinar Ilimi ta Jihar Katsina, Zainab Musa Musawa, ta yaba wa tasirin shirin, inda ta ce, “Wannan horon yana da muhimmanci wajen canza yadda ake kallon ilimi a Katsina.
“Ta hanyar ba da horo ga malamai 100, muna gina ginshikin canji mai ɗorewa a tsarin ilimi na mu.
“Wannan haɗin gwiwa da Athena Centre da Golden Links zai inganta harkokin ilimi musamman fannin kimiyya da fasahar koyarwa.”
A nasa ɓangaren, Golden Links Educational Services, wanda ya taimaka wajen bayar da horon, ya jaddada cewa, “Wannan horon yana nuna mafi kyawun hanyoyin koyarwa na duniya, inda yake horar da malamai hanyoyin aikin da za su taimaka musu su wajen tafiya da zamani.
Chidoka ya kuma yaba wa Gwamna da Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina kan samar da wuraren horo da tabbatar da nasararsa.
Bayan wannan nasarar, Cibiyar Athena tana shirin faɗaɗa wannan horo zuwa dukkanin jihohi 36, inda za a horar da malamai 10,000 a cikin watanni shida masu zuwa.
Haka kuma Athena na shirin samar da shiri mai faɗi domin horar da dubban malamai da miliyoyin ɗalibai a duk faɗin Najeriya.