✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 20 sun mutu, 66 sun jikkata a harin da Isra’ila ta kai Lebanon

Wasu hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai tsakiyar Beirut a ranar Asabar sun kashe aƙalla mutane 20 cewar Ma’aikatar Lafiyar Lebanon. Lamarin na zuwa…

Wasu hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai tsakiyar Beirut a ranar Asabar sun kashe aƙalla mutane 20 cewar Ma’aikatar Lafiyar Lebanon.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin wasu hare-haren a birnin Beirut da a baya ba’a saba gani ba a kai a kai, ba tare da wani gargaɗi daga Isra’ilan ba, yayin da ɓangaren diplomasiyya ke faɗi tashin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce, mutane 66 suka jikkata sakamakon harin, wanda shi ne hari na huɗu a tsakiyar Beirut a ƙasa da mako guda.

Harin na baya bayan nan da aka kai da misalin ƙarfe 4 na asuba, ya yi fatafata da wani ginin bene mai hawa 8 a tsakiyar Beirut.

Rincabewar rikicin ya zo ne, bayan da wakilin Amurka Amos Hochstein ya ziyarci yankin domin neman cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, da zai kai ga ƙarshen watannin da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin Isra’ila da Hezbollah da ya rikide ya zama gagarumin yaƙi.

Hare-haren Isra’ila sun kashe aƙalla ƙarin mutum 25 a faɗin Lebanon a kwanaki uku da suka gabata, abin da ya kai jimillar mutanen da aka kashe tun daga Oktoban bara zuwa 3,670 sannan adadin waɗanda aka jikkata zuwa 15,413, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon.

Hakazalika faɗan ya ɗaiɗaita kimanin mutane milyan 1 da dubu 200, ko kwatan mutanen Lebanon baki ɗaya.

A ɓangaren Isra’ila kuwa, kimanin sojoji 90 da kusan farar hula 50 ne suka mutu har lahira, sakamakon Ruwan bama-bamai a Arewacin Israila.