✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58

Falasdinawa 50,810 Isra'ila ta kashe a a Gaza wasu 115,688 kuma sun samu raunuka tun ranar 7 ga Oktoba, 2023

Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.

Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa gare su ba ta hanyar motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan tsaron farar hula.

Isra’ila ta kashe mutane 1,449 tare da jikkata wasu 3,647 tun bayan da ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 18 ga Maris, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ta kara da cewa yawan Falasdinawa da aka kashe a yakin Isra’ila a Gaza zuwa 50,810, wasu 115,688 kuma sun samu raunuka tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.