Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 tare da jikkata wasu 69 a cikin awa 24 a yankin Gaza, inda ta kai harin sama a wani asibiti da ke yankin Khan Younis.
Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta sanar cewa jiragen Isra’ila sun kashe wani jami’in lafiya tare da jikkata wasu tara a Asibitin Kuwaiti da ke yankin Al-Musawi da ke Khan birnin Younis da ke Gabashin Gaza.
Mai magana da yawun asibitin, Saber Mohammed, ya bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su sun hada da marasa lafiya da kuma jami’an kiwon lafiya.
Hakan na zuwa ne a yayin da daruwan marubuta ’yan kasar Isra’ila suka shiga gangamin kin gwamnatin kasar tasu da ta dakatar da yakin da take yi a Gaza.
Isra’ila ba ta uffan a game da harin ba a halin yanzu, amma wasu rahotanni sun nuna jami’an tsaronta sun yi awon gaba da wasu Palasdinawa 14 a yankin Yamamcin Kogin Jordan.
- Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a Kano
- Sojoji sun ceto mafiya 16 da aka yi garkuwa da wasu a Filato
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato
Ofishin Kula da Fursunoni na Palasdinawa ya bayyana cewa yanacin mutanen an kama su ne a yankin Birnin Kudu, inda aka kama mutum uku a unguwar al-Issawiyya da ke Gabashin Birnin Kudus da wasu uku a garin Anata.
A yankin Ramallah kuma na jami’an Isra’ila sun kama Palasinawa uku a garin Al-Mazarra’a Ash-Sharqiya da kuma wani mutum guda a kauyen Kobar.
Sun kuma kama wani mutum guda a unguwar Ezbet al-Jarad da ke birin Tulkarem da wani guda kuma a Ezbet al-Tayah.A yankin Nablu kuma Isra’ila ta kama Palasdinawa uku a yankunan Beit Furik da kuma birnin Nablus.