Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi watsi da ƙudirin dokar sake fasalin haraji, tare da gargaɗin cewa yana barazana ga haɗin kan ƙasa.
Ƙungiyar ta soki yadda aka aiwatar da ita, inda ta yi zargin cewa an mayar da masu ruwa da tsaki ciki har da mambobin majalisar tattalin arzikin kasa a gefe yayin gudanar da aikin.
- Mutum 20 sun mutu, 66 sun jikkata a harin da Isra’ila ta kai Lebanon
- Mun bai wa jami’anmu umarnin bincikar gwamnonin da ke kan mulki — EFCC
Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin amintattu na karo na biyu na shekara-shekara da aka gudanar a Abuja.
Kungiyar ta yabawa kungiyar gwamnonin jihohin Arewa da kuma majalisar sarakunan arewacin Najeriya da suka nuna adawa da kudurin, inda suka bayyana matsayarsu a matsayin ‘yan kishin kasa, tare da yin kira ga ‘yan siyasar Arewa a majalisar dokokin kasar da su tofa albarkacin bakinsu.
Taron ya yi nuni da cewa,“a halin da ake ciki yanzu, dokar sake fasalin haraji an yi shi ne da nufin tursasawa ’yan kasar, kuma hakan barazana ce ga hadin kanmu da hadin kan kasa.
“Taron ya ci gaba da jawo hankulan mutane kan hanyar da ba ta dace ba da kuma yadda aka sanya dokar sake fasalin haraji a kan al’umma, ba tare da ba da damar shigar da masu ruwa da tsaki ba, kamar yadda ya sanya mambobin majalisar tattalin arzikin kasa cikin duhu.
“Majalisar, ta yi Allah-wadai da kakkausar murya, da irin hasarar murya da aka yi a kan wannan batu na yawan zababbun ’yan siyasa da suka fito daga yankin, tare da yi musu gargadi da kakkausar murya.
Kungiyar ta NEF ta bukaci ’yan Arewa da su ƙara taka tsan-tsan wajen kare haƙƙinsu, musamman a lokacin zaɓe, ta kuma yi gargaɗin cewa kada su faɗa cikin maguɗin shugabanni marasa kishin ƙasa.