Ɗaya daga cikin fitattun shugabannin addini kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Alhaji Jafaru Makarfi ya riga mu gidan gaskiya.
Garkuwan Zazzau, Alhaji Suleiman Abdulkadir wanda ya fitar da sanarwa a madadin iyalansa, ya ce Alhaji Makarfi ya rasu ne a ranar Asabar da daddare a Jihar Kaduna bayan shafe shekaru 93 a doron ƙasa.
- Dokar sake fasalin haraji na barazana ga haɗin kan ƙasa — Dattawan Arewa
- Mutum 20 sun mutu, 66 sun jikkata a harin da Isra’ila ta kai Lebanon
Ya bayyana cewa za a yi jana’izar mamacin a Masallacin Sultan Bello da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadin nan.
Marigayi Makarfi wanda sanannen mutum ne a cikin al’ummar Musulmi a Najeriya, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Kaduna.
Haka kuma, marigayin ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishina a tsohuwar Jihar Kaduna.
Kazalika, Alhaji Makarfi ya yi fice a Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) inda ya shafe tsawon shekaru 40 yana aikin da ya soma a shekarar 1950.
Alhaji Makarfi ya rasu ya bar ’ya’ya shida kamar yadda sanarwar da Garkuwan Zazzau ya fitar ta bayyana.