Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah-wadai da matsayin da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Filato da wasu kungiyoyi suka dauka kan batun sake gina babbar kasuwar Jos.
JNI wacce ke karkashin jagorancin Sarkin Wase, Dokta Muhammad Sambo Haruna, a jihar ta Filato, ta bayyana haka ne a martaninta ga CAN din kan batun sake gina kasuwar.
- Babbar Kasuwar Jos mallakar Gwamnatin Filato ce —Lalong
- Matsalar tsaro: JNI ta bukaci Musulmi su dukufa addu’o’i na musamman
An yi ta cece-kuce kan ko za a gina kasuwar ko kuma ba za a yi ba biyo bayan yarjejeniyar da Gwamnatin jihar ta kulla da Bankin Jaiz.
Yarjejeniyar, a cewar Gwamnatin jihar ita ce ta samar da kudin gudanar da aikin, lamarin da CAN ta ce ya kamata a dakatar da shi.
Kungiyar ta JNI a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakatarenta na Jihar, Salem Musa Umar, ta ce kalaman abun kyama ne da kuma tunzura al’ummar Musulmin jihar sannan kuma cin mutunci ne ga addinin Musulunci.
Sanarwar ta ce, “Babban abin da ya fi damun mu shi ne faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani inda wani ke bayani a karkashin reshen wata kungiyar da ta kira kanta ta Masu Kishin Kiristoci ta Jihar Filato
“Muna mamakin tun yadda aikin sake gina babbar Kasuwar Jos ya koma batun addini, cewa kungiyoyin addini za su yi amfani da ita wajen jefa kalamai na cin zarafin Musulmi da Musulunci?” inji sanarwar.
Kungiyar JNI ta bayyana kaduwa da cewa wanda a cikin bidiyon ya bayyana Musulmi a matsayin ’yan ta’adda kuma ya zarge su da kona kasuwar a lokacin da ta ce rabin masu shaguna da masu gudanar da kasuwanci a ciki Musulmai ne.
JNI ta ce ta tsaya ba don kawai bankin Jaiz na da hannu a ciki ba, ta yi imani da inganci da bukatuwar ganin babbar kasuwar ta dawo aiki domin amfanin kowa da kowa a jihar.