✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya kira shugabannin yankin domin yin taro game da rikicin.

Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato.

Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu.

Rikicin ya ɓarke ne a dare ranar Talata, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba.

Lawan Chizo, wani jigo a ƙungiyar tsaro ta sa-kai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun shiga tsakani don kwantar da tarzomar.

Ya ce rikicin ya haɗa da mambobin Sara-Suka daga Anguwan Rogo da Yantifa, waɗanda ke rikici da juna da daɗewa.

Duk da cewa har yanzu jama’a na cikin fargaba, Chizo ya tabbatar da cewa zaman lafiya ya wanzu a yankin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya kira taron gaggawa tsakanin shugabannin al’ummomin yankin domin kawo ƙarshen rikicin.

Wannan rikici ya faru ne kwana biyu bayan wani faɗa da ya ɓarke a harabar Masallacin Al-Mohap, inda aka kashe mutum uku daga cikin ‘yan Sara-Suka.