Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello tare da mambobin Kwamitin Babban Taron Jam’iyyar na Kasa sun sallami Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata James Akpanudoedehe daga mukaminsa.
Rikicin Shugabancin APC ya dauki sabon salo ne a ranar Alhamis, washegarin da Sanata James Akpanudoedehe ya ci gaba da aiki, ya kuma jagoranci fara sayar da takardun neman tsayawa takarar kujerun shugabancin jam’iyyar.
- Matar tsohon Gwamnan Anambra ta tsinka wa matar Ojukwu mari a wajen rantsuwa
- An rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon Gwamnan Anambra
A matsayinsa na Sakataren Jam’iyya, Sanata James Akpanudoedehe, shi ne mutumin da ke jagorantar kwamitin gudanarwar APC a duk lokacin da Shugaban Riko da Kwamitin Babban Taron Jam’iyyar, wato Gwmanan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ba ya nan.
Amma Gwamna Abubakar Sani Bello, wanda a baya ya yi ikirarin zama Mukaddashin Shugaban Rikon Jam’iyyar, da sauran mambobin kwamitin babban taron mai mutum 10 wadanda ke gudanar da jam’iyyar tun daga watan Yunin 2020, sun sanar cewa sun yanke kauna daga irin kamun ludayin Sanata Akpanudoedehe a jam’iyyar.
Sanata James Akpanudeohehe ya fara shiga tsaka-mai-wuya ne a makon jiya bayan rana tsaka Bello da wasu mukarrabansa sun yi ikirarin karbe ragamar shugabancin jam’iyyar, har suka gudanar ta taron gaggawa kan shirye-shiryen babban taron, a yayin da Shugaban Rikon Jam’iyyar, Mai Mala Buni, ke kasar waje.
Sanarwar da suka fitar na dauke da sa hannun Gwamna Bello da sauran mambobin kwamitin — Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ken Nnamani; Sanata Yususf Abubakar Yususf, Farfesa Tahir Mamman, David Lyon, Akinremi Olaide, Barista Ismaeel Ahmed, Dokta James Lalu, da kuma Stella Okotete.
A halin yanzu dai duk mambobin kwamitin rikon, in banda Mai Mala Buni, sun riga sun rattaba hannu kan takardar korar Sanata Akpanudeodehe ba.
Kawo yanzu dai ba a kai ga jin ta bakin Sanat Akpanudoedehe ba.