✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja

Rundunar ta ce daga baya al'amura sun daidaita a yankin.

Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu.

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ta ce ’yan shi’a sun kai wa jami’an tsaro hari da bindigogi, duwatsu, da wasu makamai.

A sakamakon haka, aka tura ƙarin dakaru domin kwantar da tarzomar.

“Kwamishinan ’yan sanda, CP Ajao Saka Adewale, ya yi tir da wannan hari da aka kai wa jami’an tsaro,” in ji kakakin rundunar, Josephine Adeh.

“Ana ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.”

Wani ganau da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana yadda rikicin ya ɓarke.

“Ina wucewa kawai sai naga taron jama’a suna jifan jami’an tsaro. Ba zato ba tsammani, sai aka fara jin harbin bindiga, mutane suka fara gudu,” in ji shi.

Jami’an tsaro sun tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin, sannan sun buƙaci jama’a su zauna lafiya tare da bayar da rahoton duk wank abun zargi.