✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata mata ta yanke mazakutar mijinta

Wata matar aure da ake zargi da yanke mazakutar mijinta a yankin Tella a karamar hukumar Gassol a jihar Taraba ta shiga hannun hukuma. Matar…

Wata matar aure da ake zargi da yanke mazakutar mijinta a yankin Tella a karamar hukumar Gassol a jihar Taraba ta shiga hannun hukuma.

Matar ‘yar shekara 25 ta yanke mazakutar mijin nata ne da wuka a lokacin da yake barci a ranar Talata, abin daya sa shi kurma ihun da ya sa ‘yan uwansa zuwa cikin gaggawa suka iske shi jina-jina ta yanke masa al’aurarsa.

“Mun same shi cikin jini a zaune a gefen gado rike da wuka mai kaifi, wadda ta yi amfani da ita wajen yanke mazakutar dan uwana, inji dan uwan mijin.

“Kadan ya rage mutanen da suka zuciya ba su kashe ta ba, saboda tana dauke da juna biyu, hakan ne ya sa manya suka shiga tsakani suka kira ‘yan sanda”, inji shi.

Ya ce an kai dan uwan nasa Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jalingo cikin gaggawa inda aka tsayar da jinin da ke ta malala daga inda ta yi masa raunin.

Likitan da ke kula da mutumin, Dakta Kyantiki Peter Adamu ya shaida wa Aminiya cewa, “Majinyaci zai iya warkewa ya rayu dari bisa dari”.

Wani dan uwan majinyancin, ya ce za su mayar da shi Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke jihar Gombe.

Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da lamarin, ya ce sun kama matar kuma suna kan gudanar da bincike.