✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wasu mata sun sha da kyar a wajen zabe a Kano

Da kyar jami’an tsaro suka kwato matan daga hannun fusatattun mutane.

Wata mata da ba a bayyana sunanta ba ta sha da kyar sakamakon daga takardar zabe da ta yi bayan ta kada kuri’arta a wata mazabar unguwar Giginyu da ke Karamar Hukumar Tarauni.

Rahotanni sun bayyana cewa tunda farko matar ta yi wa wakilan jam’iyyu daban-daban alkawarin zabar su, don haka lokacin da ta nuna abin da ta zaba hakan ya fusata sauran wakilan jam’iyyu inda suka yi ca akanta.

Daga karshe dai jami’an tsaro sun yi nasarar tserar da ita.

Haka kuma, wasu mata biyu – Amina da Zubaida – sun sha da kyar sakamakon zarginsu da sayen kuri’a a mazabar.

Rahotanni sun bayyana cewa matan suna ta bibiyar matan da ke rumfar zaben suna neman sayen kuri’arsu.

Wannan lamari dai kamar yadda wakiliyarmu ta ruwaito ya fusata mutanen da ke kokarin kada kuri’arsu a mazabar inda suka far musu da duka.

Daga baya dai jami’an tsaro sun tserar da su daga hannun fusatattun mutanen.

%d bloggers like this: