Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bar wasu masu katin zabe na wucin gadi su kada kuri’a a zaben gwamnoni da majalisun dokokin jiha da ke tafe ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ba da umarnin ne bayan wasu ’yan Najeriya biyu, masu suna Kofoworola Olusegun da kuma Wilson Allwell, sun shigar da karar neman INEC ta bari masu katin zabe na wucin-gadi su yi zaben da ke tafe.
“Masu kara na da ’yancin amfani da katin zabensu na wucin-gadi a zabe mai zuwa tunda sun riga sun yi abin da ya rataya a kansu na rajistar zabe kuma bayanansu sun fito a rumbun adana bayanai da sauran takardun zabe da INEC ta wallafa,” in ji alkalin.
“Tunda ba a matsayin wakilci aka kawo karar ba, ba ni da hurumin amsa bukata ta uku, ta barin duk halastattun masu katin zabe na wucin-gadi su kada kuri’a,” in ji alkalin.
Ya ce hatta sashe na 47 na dokar zabe, katin zabe kawai ya yi magana, bai ce sai na dindindin ba.
A cewarsa tun da har wadanda yake wakilta sun yi duk abin da doka ta ce na yin rajista, amma har lokacin ba da katin dindindin ya wuce ba su samu nasu ba, to ya kamata a bari su yi zabe.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a halin da ake ciki, wajibi ne bin umarnin kotun ga INEC, har sai idan kotun daukaka kara ta jingine hukuncin.