✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatanmu na kai wa ‘yan bindiga bayanai —Jami’ar FUDMA

Hukumomin tsaro sun fara bincike kan ma'aikatan jami'ar da ake zargin sun yi wa ’yan bindiga leken asiri

Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Bichi, ya yi zargin cewa wasu daga cikin ma’aikatan jami’ar na yi wa ’yan bindiga leken asiri.

Farfesa Armaya’u Bichi ya yi wannan zargi ne a yayin ganawarsa da manema labarai, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

’Yan bindiga suna ta kai hare-hare a yankin, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan jami’ar da kuma iyalansu.

Mako guda da ya gabata ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan Dakta Tiri Gyan David, Shugaban Tsangayar Tattalin Arzikin Noma da Raya Karkara na FUDMA, inda suka kashe shi tare da sace ’ya’yansa.

A yayin da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Talata, Bichi ya ce an bai wa wata hukumar tsaro damar ta tuntubi wasu ma’aikatan jami’an da ake zargin don ta bincike su.

A cewar shugaban jami’ar, hukumomin makarantar suna yin duk mai yiwuwa don hana sake afkuwar irin haka, amma lamarin sai ƙara ta’azzara yake yi.

Bichi ya ce, “Wannan batu na masu ba da labari abin damuwa ne, don haka, muna binciken waɗanda muke zargin su da bayar da bayanan abokan aikinsu da ɗalibansu.

“Mun gano su, kuma mun miƙa bayanansu ga ɗaya daga cikin hukumomin tsaro domin gudanar da bincike.

“Amma zuwa yanzu ba mu ji komai daga jami’an tsaro ba.

“Waɗanda ake zargin ma’aikatanmu ne kuna muna da ƙwararan dalilai na zargin su da kasancewa masu ba da bayanai ga ’yan bindigar,” in ji Shugaban jami’ar.

Da aka tuntuɓi ’yan sanda, sun ce ba su da masaniya kan wannan batu amma sun yi alƙawarin ci gaba da bincike kan lamarin.