✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasikar Kurciya

KHALID IMAM ya rubuta wannan wake mai taken “Wasikar Kurciya” wanda za mu iya cewa salo ne ya dauka tamkar na marigayi Malam Sa’adu Zungur,…

KHALID IMAM ya rubuta wannan wake mai taken “Wasikar Kurciya” wanda za mu iya cewa salo ne ya dauka tamkar na marigayi Malam Sa’adu Zungur, wanda shekaru kusan 60 da suka gabata ya wallafa mashahurin wakensa mai taken “Arewa: Jamhuriyya Ko Mulukiyya?” Waken Khalid na kunshe ta tunasarwa da fadakarwa ga al’ummarmu ta yau, kamar dai yadda Malam Sa’adu ya yi a zamaninsa.

 

Baba Zungur ya faɗi gaskiya,

Na gaida Sa’adu  mazan jiya.

 

A batu nasa ba na tankiya,

Na miƙa wuya na ji gaskiya.

 

Na ji ya ce  ribar duniya,

Neman ilimi da barin tsiya.

 

Jahilci bai sa arziki,

Sai ƙarya sai sharholiya.

 

Karya ce ke neman ado,

Da baƙin gyauto ko rawaya.

 

Jan baki daudau baki nata,

Tai muƙwi ta sanya makawuya.

 

Mai ƙarya ce masa ɗan dako,

Mai dara ja duk annakiya.

 

Karya ka buƙatar zabiya,

Ko sanƙira maras gaskiya.

 

Jahilai aikinsu jagaliya,

Dare rana har safiya.

 

Gaskiya ba ta yin fariya,

Ko tsoron ai mata dariya.

 

Gaskiya fadarta akwai zuma,

Dubulan alkaki nakiya.

 

Wanda duk ya riƙeta da gaskiya,

Ba shi ba kunyar duniya

 

Ilimi jarin ne gaskiya,

Mai shi ba ai masa dariya.

 

Da shi aka mulkin duniya,

Daɗin saukuwa sai goɗiya.

Yau Bahaushe ba shi da zuciya,

Sai barace-barace a duniya.

 

’Yan mata sai ƙaryar tsiya,

Samarin yau sai fariya.

 

Sun bar hanya gargajiya,

Ci gabansu na mai haka rijiya.

 

Shugabanni sai son zuciya,

Burinsu su mallaki dukiya

 

Rumbu na ƙasa sun wawashe,

Sata murjanin gafiya.

 

Don ba sa tsoron Mai Duka,

Talakawa yau sai shan wuya.

 

A Arewa zumunci babu yau,

Amana kira ta marainiya.

 

Kin Allah ya ci lakarmu duk,

Sai ƙarya ba ma gaskiya.

 

A ƙasa ba mai ƙaunarmu yau,

Wai tuwo sai dai mu ci ba miya.

 

Kadangare bai samun yai gida,

Sai bango ya tsage gaskiya.

 

Gaiwa sunanmu a yau duka,

Ba mu son junanmu gaba ɗaya

 

Mun zan barorin ’yan Kudu,

Da ilimi suka fi mu a kwalliya.

 

Yau a Arewa ake satar mutum,

Wai kawai a samu na shan giya

 

Kasuwanci noma sun mutu,

Son jiki duk yai mana karkiya.

Sai  bacci sai mu yi kwanciya,

Shi ne burinmu a ƙungiya.

 

Yan siyasa sun raba kanmu duk,

Ba mu cin riba sai shan wuya.

 

Ba mu son junan mu da gaskiya,

Sai shirme sai sharholiya.

 

‘Yan boko sun mana sakiya,

Sun raba mu da al’adun jiya.

 

Makuwa ko mun yi muna gani,

Mun nausa daji na fagainiya.

 

’Yan Arewa mu daina fagamniya,

Duk mu dawo turbar gaskiya.

 

In an ce waƙa wa ya yi?

To ku ce Khalid maras turjiya

 

Ni lmam burina duniya,

Na kaunaci Khairul Anbiya.

 

Nan zan ɗiga aya in tsaya,

Na ida da wasiƙar kurciya.