Wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sun harbe basaraken yankin Obelle da ke Karamar Hukumar Emohua ta Jihar Ribas, Cif Ferdinand Dabiri, har lahira a yayin da ake tsaka da wani taro.
Cif Ferdinand da aka kashe ana tsaka da taron sarakunan yankin, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakuna ta karamar hukumar a ranar Asabar.
Harin ya tilasta wa sarakunan da suka halarci zaman tserewa domin kubutar da rayuwarsu, a yayin da al’ummar yankin suka shiga zullumi.
Dan mamacin mai suna Joseph Dabiri, ya shaida wa manema labarai cewa, “Na samu labarin cewa wani matashi ne ya je wajen mahaifina ya harbe shi sau biyu da bindiga a kauyen Umuwoka, sannan ya tsere.”
- ’Yan bindiga sun sace ’yan kasuwa 4 sun wawushe shaguna a Bauchi
- Gwamnan Katsina ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota a hanyar Daura
Joseph ya bayyana cewa sun kai rahoton kisan ga Babban Ofishin ’Yan Sanda na yankin Rumuji, yana mai kira da a yi musu adalci.
Zuwa lokacin da muka samu wannan rahoto dai rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa game da lamarin ba.
Kisan gillar da aka yi masa ya zo ne bayan ’yan sanda sun tarwatsa fadin wasu gungun kungiyoyin asiri biyu da ba sa ga maciji da juna a Fatakwal, babban birnin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa mambobin daya daga cikin kungiyoyin sun hanyarsu ta zuwa babbar harabar Jami’ar Fatakwal domin far wa abokan hamayyarsu ne bangarorin biyu suka yi arangama a hanya, inda suka fara musayar wuta.
Arangamar ta tilasta wa masu shaguna da mutanen gari tserewa, amma aka yi sa’a ’yan sanda suka kawo dauki suka fatattaki bata-garin.
Kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko ta sanar da cewa mutum uku daga cikin wadanda ake zargi sun shiga hannu kuma an kwace bindigar hannu guda daya a hannunsu.
Jami’ar ta bayyana cewa rundunar tana ci gaba da bincike domin kamo ragowar masu hannu a tayar da zaune tsayen.